Kwacen mota ya fi gyaran karaya kawo kudi - Abdullahi Mudi

Kwacen mota ya fi gyaran karaya kawo kudi - Abdullahi Mudi

Abdullahi Mudi, Wani matashi dan shekaru 25 dake gyaran karaya, ya ce ya fi samun kudi da kwacen mota a kan sana'ar sa ta dorin karaya. Matashin ya fadi haka ne yayin da jami'an 'yan sanda na rundunar IRT suka kama shi a maboyar sa dake Lokoja, jihar Kogi.

Daga cikin wadanda jami'an suka kama bayan Mudi, akwai Christopher Ilia, maigadi a wata ma'aikata dake Abuja.

Mutanen biyu na daga cikin wata tawagar 'yan fashi da makami ta mutane hudu da suka kware da kwacen manyan motoci a Lagos da Abuja.

Mudi ya ce mahaifinsa ya koya masa gyaran karaya kafin ya rasu, amma daga baya ya koma fashin manyan motoci domin ta fi kawo kudi. Matashin ya ce sun kwaci manyan motoci 30 tare da sace wasu 20 a Legas.

Ya kara da cewar sun fi yin kwacen motoci a unguwannin Lekki da Ikeja da Surelere dake garin Legas.

Kwacen mota ya fi gyaran karaya kawo kudi - Abdullahi Mudi

Abdullahi Mudi da abokinsa da suke fashi tare
Source: Facebook

Dukkan wadanda aka kama na tsare a ofishin rundunar 'yan sandan IRT dake Abuja.

A wani labarin na Legit.ng mai kama da wannan, kun ji cewar An kama wani tsohon boka, Samuel Hunsu, mai shekaru 85, a garin Abeokuta, jihar Ogun da danyun zuciyoyin mutane.

Yayin bajakolin Hunsu ga manema labarai, jami'an 'yan sanda na ofishin shiyya ta 2 dake Onikan a jihar Legas, sun ce dattijon ya amince da amfani da sassan jikin mutane domin tsafin kudi.

DUBA WANNAN: Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas

Sai dai, Hunsu ya ce wani mutum ne mai suna Abiodun ya kawo masa zuciyar domin a yi masa tsafin samun kudi.

A cewar dattijo Hunsu, "Abiodun ne ya kawo min zuciyar bayan ya tuntube ni domin hada masa tsafin kudi kuma na fada masa abubuwan ake bukata. Nima nayi mamakin ganinsa da zuciyar mutum. Sai da na tambaye shi inda ya samo zuciyar mutum, amma sai yace ya ciro ta ne a jikin wani barawo da aka kashe a jihar Ogun. Bayan ya tafi ne sai na adana zuciyar cikin wasu sinadarai don kar ta lalace, har zuwa lokacin da zai dawo. Ban san Abiodun ba kuma ban san inda yake da zama ba. Ni dai kawai ya ce min ya zo wurina ne tun daga jihar Kwara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel