Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas

Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas

- Daya daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram mafi hatsari, Umar Abdulmalik, ya shiga hannun jami'an rundunar 'yan sanda

- Jami'an rundunar 'yan sanda ta IRT, karkashin jagorancin Abba kyari ne suka kama Umar a Legas bayan musayar wuta

- An kama Umar din ne a yankin Ibafo dake garin Legas inda yake zaman jinya bayan samun raunukan harbin bindiga daga yunkurinkama shi a Abuja

Hotunan, Umar Abdulmalik, babban kwamanda a kungiyar Boko Haram tare da wasu gungun 'yan fashi da jami'a rudunar 'yan sanda ta IRT suka kama a Legas ranar Alhamis ya bayyana.

Umar, daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da ake zargi da daukan nauyin harin hare-haren bam na Kuje da Nyanya dake Abuja a shekarar 2015, ya shiga hannu.

Kazalika ana zargin kwamandan da kisan jami'an 'yan sanda biyu a ofishin hukumar 'yan sanda na Lugbe da Gwagwalada da kuma jagorancin fashi a bankuna a jihohin Edo da Ondo.

Jam'ian rundunar 'yan sanda ta IRT ne karkashin jagorancin DCP Abba Kyari suka kama kwamandan tare da wasu gungun 'yan fashi a yankin Ifabo dake garin Legas bayan musayar wuta.

Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas
Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama tare da 'yan fashi a Legas
Asali: Facebook

Majiyar mu ta ce Umar ya samu tsira da raunuka daga yunkurin kama shi da jami'an 'yan sanda suka yi a Abuja, sati uku da suka wuce. Sai dai, an kama hudu daga cikin yaransa da bindigu 4 samfurin AK-47 da alburusai masu yawa.

Umar ya gudu yankin zuwa Ibafo dake garin Legas inda yake zaman jinya daga raunukan da ya samu a musayar wuta da jami'an tsaro a Abuja. Sai da aka yi musayar wuta da jami'an rundunar IRT kafin su kai ga kama Umar.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

A cewar majiyar mu, Umar ne ya jagoranci harin da mayakan Boko Haram suka kai gidan yari na Kuje inda har ya rasa daya daga cikin idanunsa. Fursuna fiye da 100 ne suka tsere daga gidan yarin sakamakon harin.

Jam'ian rundunar 'yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike domin kama ragowar 'yan kungiyar Boko Haram dake aiki tare da Umar.

Dukkan wadanda suka shiga hannu sun amsa laifin aikata aiyukan ta'addanci. Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel