Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya ce ko kadan baya tsoron wadanda ke kokarin yi masa zagon kasa dangane da zaben 2019 a cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ya ce Allah kawai ya ke tsoro da kuma shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a jiya, Juma'a a yayin da ya ke karbar wasikar goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben Fabrairun 2019 daga Allied People’s Movement (APM).

A yayin da ya ke karbar wasikar daga dan takarar gwamna na APM, Hon. Abdulkabir Akinlade a sakatariyar APC da ke Abiola Way a Abeokuta, gwamnan ya kuma sake jadada cewa shugabanin jam'iyyar APC na jihar Ogun karkashin jagorancin Cif Derin Adebiyi za su cika wa'adin su na shekaru hudu.

Ba mu tsoron komai sai Allah da kuma Shugaba Buhari - Gwamnan APC
Ba mu tsoron komai sai Allah da kuma Shugaba Buhari - Gwamnan APC
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

Ya yi wannan maganar ne kwanaki kadan bayan Kwamitin ayyuka na uwar jam'iyyar ta zabi sabbin shugabanin rikon kwarya a jihar sakamakon ruguje shugabanin jam'iyyar da tayi a ranar Lahadi da ya gabata.

Gwamnan ya ce Oshiomole ya bata lokacinsa ne kawai domin sai Adebiyi ya karasa wa'addin mulkinsa.

Ga wasu daga cikin kalamen Amosun: "Ya kamata a ce kun san ni a yanzu. Ina mutunta mutane amma Allah kadai nake tsoro. Saboda haka babu abinda zai sa muyi shiru dominba tsoro mu keyi ba.

"Ba mu tsoron su, dukkansu ba su bamu tsoro. Allah kadai muke tsoro sai kuma Shugaba Muhammadu Buhari.

"Mu 'yan adam ne. Ba mu ne Allah ba shi yasa muke son mu fada musu cewa a wannan zaben mai zuwa a jihar Ogun, wanda al'umma suka zaba ne zai yi mulki.

"Sai mu nuna musu ta hanyar kuri'un mu. Idan suna neman jihar da za su lalata su dena tunanin Ogun. A shirye muke mu tunkare su.

"Mun kyale su ne kawai saboda darajar Shugaba Muhammadu Buhari. Idan ba domin shugaban kasa ba, mun san matakin da za mu dauka a kan su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164