Interpol ta bayar da umurnin a kamo Diezani Allison-Madueke

Interpol ta bayar da umurnin a kamo Diezani Allison-Madueke

'Yan sandan kasa da kasa na Interpol ta bayar da umurnin kamo tsohuwar Ministan man fetur na Najeriya, Diezani Allison-Madueke sakamakon bukatar da gwamnatin Najeriya ta shigar da mika ta ga kasar domin fuskantar shari'a.

Wannan umurnin yana nufin dukkan kasashen da ke aiki tare da Interpol za su damke tsohuwar Ministan a duk inda suka gan ta a iyakar kasashen su.

Madueke dai ta dade tana buya a birnin Landan da ke kasar Ingila na tsawon shekaru uku.

Punch ta ruwaito cewa a tare da takardan neman dawo da tsohuwar Ministan zuwa Najeriya akwai takardan kama ta da mai shari'a Valentine Ashi na babban kotun tarayya da ke Abuja ya bayar a ranar 4 ga watan Nuwamba.

Interpol ta bayar da umurnin a kamo Diezani

Interpol ta bayar da umurnin a kamo Diezani
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Kotun ta bawa Sufeta Janar na 'yan sanda, Ciyaman din hukumar EFCC, shugaban hukumar SSS da sauran shugabanin hukumomin tsari su damko tsohuwar ministan na man fetur a duk inda su kayi karo da ita.

Majiyar ta ce, "Mun bi dukkan ka'idojin da suka dace kuma Interpol ta bayar da umurnin kama Allison-Madueke. Wannan ya nuna shirin dawo da ita gida Najeriya domin fuskantar shari'a ya fara aiki kenan kuma akwai yiwuwar 'yan sandan Interpol na Ingila ko wata kasar daban na duniya za ta iya kama ta a mika ta ga Najeriya."

Sai dai a yayin da aka duba shafin internet na Interpol, ba a ga sunan wadda ake zargin ba cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Mutane biyu kawai daga Najeriya Ehirobo Nathaniel, 53, da Ernest Kenel, 49 wadanda ake nema saboda damfarar kudi aka gani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel