Kukan dadi: Mazauna Maiduguri sun yi korafi da samun wutar lantarki

Kukan dadi: Mazauna Maiduguri sun yi korafi da samun wutar lantarki

Mazauna garin Maiduguri a jihar Borno sun yi korafi a kan samun wutar lantarki ta fiye da sa'o'i 24 da kamfanin raba hasken wutar lantarki na Yola (YEDC) ke basu.

Da suke magana da da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), mazauna garin sun bayyana samun wutar da cewar ya yi yawa kuma ya jawo kamfanin YEDC na cajar su kudi mai yawa a karshen wata.

Ibrahim Suleiman, mazaunin unguwar Bolori, ya roki YEDC da ya rage tsawon lokacin da yake basu wutar lantarki.

Kukan dadi: Mazauna Maiduguri sun yi korafi da samun wutar lantarki

Kukan dadi: Mazauna Maiduguri sun yi korafi da samun wutar lantarki
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

"Muna kira ga YEDC da ya koma tsarin bayar da wuta na sa'o'i 12 a rana kamar yadda suke yi a baya," a cewar sa.

Sannan ya cigaba da cewa, "ina yin aiki daga karfe 7:00 na safe zuwa 4:00 na yamma kuma bana amfani da wutar lantarki sai na koma gida, amma duk da haka a karshen wata zasu aiko min da takardar wuta dauke da kudi mai yawa. Gaskiya babu adalci a cikin tsarin.

Mazauna garin sun shaidawa NAN cewar tsadar wutar da suke samu ya yi yawa kuma yana shafar tattalin arzikinsu.

Da yake raddi ga korafin jama'a, Usman Wakta, manajan kamfanin YEDC a Maiduguri, ya ce ba wai suna cajin masu amfani da wutar lantarki ba tare da lissafi bane.

"Yanzu muna iya bayar da hasken wutar lantarki na sa'o'i 22 kowacce rana sabanin sa'o'i 22 a baya, samun wutar ya karu, haka ma kudin da ake biya duk wata dole ya karu," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel