Rigimar duniya: An kama AIG na bogi da katin ATM 11 a Abuja

Rigimar duniya: An kama AIG na bogi da katin ATM 11 a Abuja

'Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 59 dake ci da buguzum a matsayin AIG a rundunar 'yan sanda ta kasa. An kama mutumin ne a wani banki dake unguwar Kubwa a Abuja.

An kama mutumin mai suna Olawale Olatunji dauke da katin ATM na cire kudi guda 11 da takardun cire na bankuna daban-daban har guda 10.

Da ya ke gabatar da mai laifin ga manema labarai, Bala Ciroma, kwamishinan 'yan sandan Abuja, ya ce Olatunji na damfarar mutane ta hanyar yi masu alkawarin samun kwangila a aiyukan da hukumar 'yan sanda ke yi.

Rigimar duniya: An kama AIG na bogi da katin ATM 11 a Abuja

Rigimar duniya: An kama AIG na bogi da katin ATM 11 a Abuja
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yi tsokaci kan ihun da aka yiwa Buhari yayin gabatar da kasafin kudi

A cewar Ciroma, "a ranar 10 ga watan Disamba, jami'an 'yan sanda sun kama wani mutum mai suna Olatunji dake gabatar da kansa a matsayin mataimakin babban sifeton rundunar 'yan sanda (AIG).

"Olatunji ya damfari mutane da yawa da sunan zai sama masu kwangilar a wani aiki da hukumar 'yan sanda ke yi.

"A yayin gudanar da bincike ne muka gano takardun bogi na kwangila da katin ATM na cire kudi guda 11 da takardun cire kudi na bankuna daban-daban har guda 10 da takardun kamfanoni da dama."

Sai dai Olatunji ya musanta cewar yana gabatar da kansa a matsayin AIG sannan ya ce bai taba damfarar kowa. Kazalika ya bayyana cewar takardun kamfanoni da ake magana na kamfanonin da suke harkokin kasuwanci tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel