Mataimakin Shugaban kasa ya jagorancin Zaman Majalisar Zantarwa

Mataimakin Shugaban kasa ya jagorancin Zaman Majalisar Zantarwa

A yayin da a jiya Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwashi 'yan kallo a zauren majalisar tarayya yayin gabatar da kasafin kudin kasa na 2019, Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zantarwa.

Mun samu cewa, a ranar Larabar da ta gabata Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci wani dan takaitaccen zama na majalisa cikin abinda bai wuci sa'a guda da rabi.

Zaman majalisar kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, ya fara gudana ne da misalin karfe 10.03 na safiyar jiya Laraba a zauren da ya saba gudana na Council Chamber da ke fadar shugaban kasa ta Villa a garin Abuja.

Mataimakin Shugaban kasa ya jagorancin Zaman Majalisar Zantarwa
Mataimakin Shugaban kasa ya jagorancin Zaman Majalisar Zantarwa
Asali: Depositphotos

Ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Okechukwu Enelemah, shine ya gabatar da addu'a bude taro ga mabiya addinin Kirista, yayin da Ministan Birnin tarayya, Muhammad Bello, ya yiwa mabiya addinin Islama ta su addu'ar ta bude taro.

Bayan kammala zaman majalisar, Ministoci da sauran kusoshin gwamnatin tarayya sun nufaci majalisar dokoki ta tarayya cikin tawagar shugaban kasa Buhari wajen gabatar da kasafin kudin kasar nan na shekarar badi.

KARANTA KUMA: Duk da kalubalan da muka fuskanta, Najeriya ta samu ci gaba ta kowace fuska - Buhari

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, ba bu wani rahoto dangane da ababen da aka tattauna yayin zaman majalisar biyo bayan umarnin Ministan watsa labarai, Alhaji Lai Muhammad, ya nemi a kauracewa manema labarai bayan gudanar da zaman.

Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, an yiwa shugaba Buhari ihu na nuna adawa yayin gabatar da kasafin kudin a zauren majalisa. Hakan ya janyo cecekuce a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel