Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Talata, 25 ga wata, da Laraba, 26 ga wata, da ranar Talata, 1 ga watan Janairu, a matsayin ranakun hutun kirsimeti, sabuwar shekara, da ranar dambe.

Mohammed Manga, darektan yada labarai a ma'aikatar harkokin cikin gida, ne ya fitar da wannan sanarwa a madadin gwamnatin tarayya da ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau.

Gwamnatin tarayya ta taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar kirsimeti tare da yi masa fatan yin shagulgulan biki lafiya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun kirsimeti da sabuwar shekara

Dambazau
Source: Depositphotos

Kazalika, gwamnatin tayi kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu hadin kai da kaunar juna.

DUBA WANNAN: Buhari ya halarci bikin taya Nijar murnar cika shekaru 60 da zama Jamhuriya

Dambazau ya bukaci dukkan 'yan Najeriya, na cikin gida da kasashen ketare, da su cigaba da bawa gwamnatin shugaba Buhari goyon baya a kokarin da take yi na kawo cigaba mai amfani ga kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel