Atiku: Tsofin gwamnonin PDP biyu sun koma APC a Adamawa

Atiku: Tsofin gwamnonin PDP biyu sun koma APC a Adamawa

Takarar gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Jibrilla Bindow, ta samu karin karfi bayan tsofin gwamnonin jihar biyu sun canja sheka daga PDP zuwa APC.

Tsofin gwamnonin biyu; Boni Haruna da James Ngalari, da suka mulki jihar a karkashin jam'iyyar PDP sun koma APC tare da bayyana goyon bayansu ga takarar gwamna Bindow.

Majiyar mu ta shaida mana cewar tsohon gwamna Haruna ya yanke shawarar fita daga PDP ne saboda rashin jituwar dake tsakaninsa da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Haruna ne dan takarar mataimakin Atiku lokacin da ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa a PDP a shekarar 1999 kafin daga bisani ya zama gwamna bayan Obasanjo ya zabi Atiku a matsayin mataimakinsa.

Atiku: Tsofin gwamnonin PDP biyu sun koma APC a Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa; Jibrilla Bindo
Asali: Depositphotos

Wata majiya ta ce Haruna ya raba hanya da Atiku ne saboda jin haushin yadda Atikun ya jawo aka mayar da shi abin dariya a jihar ta Adamawa.

Majiyar ta ce Bala Ngalari ya bar PDP ne saboda fushin kasa samun tikitin takara da ya yi a zaben fitar da 'yan takara da jam'iyyar ta yi a jihar.

Daya daga cikin hadiman gwamnan da ya nemi a sakaya sunansa ne ya tabbatar sanar da hakan, tare da bayyana cewar nan ba da dadewa ba tsohon gwamnan zai bayyana fitar sa daga PDP da kansa.

DUBA WANNAN: Kwace takara: Sanata Buruji ya yi karin haske a kan hukuncin kotu

Da yake tabbatar da labarin canjin shekar tsofin gwamnonin, Mista Maculey Humohashi ya ce bayan tsofin gwamnonin, tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mista Kobis Thimum Ari, ya canja sheka daga PDP zuwa APC.

Kazalika Mista Ari da kansa ya tabbatar da labarin canjin shekar sa zuwa APC. Ya ce, "tabbas na fita daga PDP na koma APC saboda ita ce jam'iyyar da take mulki don jama'a. Za a iya ganin aiyukan gwamnatin APC a ko ina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel