Gwamnati ta dauki Mata 1500 aikin karantarwa a jihar Kano
- Gwamna Ganduje ya dauki Mata 1500 aikin karantarwa a jihar Kano
- Gwamnati ta nemi habaka ingancin karatun ilimi a Kanon Dabo
- An nemi Malaman jihar Kano da su jajirce bisa aiki da nuna kwarewa gami da gogayya a makamar su ta aiki
Mun samu cewa, gwamnatin jihar Kano ta dauki Mata fiye da 1500 aikin karantarwa a yayin da ta ke ci gaba da fafutikar habaka ingancin ilimi a fadin jihar.
Shugaban karamar hukumar Dala, Alhaji Ibrahim Ali, shine ya bayyana hakan yayin bai wa wasu daga cikin Matan 21 takardun su na daukar aiki domin aikin karantarwa a shiyoyin karamar hukumar da ke cikin birnin Kanon Dabo.
Cikin wata sanarwa da sa hannun jami'in hulda da al'umma na ma'aikatar karamar hukumar Dala, Alhaji Haruna Gunduwawa, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Talata cikin birnin Kano.
Babban jami'in ya gargadi sabbin ma'aikatan akan jajircewa da tsayuwa bisa aiki domin habaka ingancin ilimi a fadin jihar kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.
Alhaji Ali ya bayyana takaicinsa dangane da yadda daukar malamai ma su nakasun cancanta da rashin gogewar aiki ta sanya jihar Kano ta afka cikin barazana da rauni na rashin tabbatar da ingataccen ilimi a fadin jihar.
A yayin haka shugaban karamar hukumar ya yabawa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje dangane da wannan hobbasa da daukar sabbin Malamai Mata fiye da 1500 cikin shekaru ukun da suka gabata.
KARANTA KUMA: Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama a garin Abuja
A nasa jawabin, babban jami'in kula da aikace-aikacen kananan hukumomi na jihar Kano, Ahmad Kado, ya nemi daukacin Malaman jihar Kano akan jajircewa bisa aiki da dabbaka managarcin horo da kwarewa a makamar su ta aiki.
Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sama da magoya bayan Kwankwasiyya 25,000 sun sauya sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC a jihar Kano.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng