Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama a garin Abuja

Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama a garin Abuja

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 20 ga watan Dasumba, zai kaddamar da wani katafaren aiki da aka kamalla ginin sa a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe International Airport da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama ta kasa da kasa da aka kammala ginin ta a filin jirgin saman da ke garin Abuja kamar yadda wani babban jami'i ya bayyana.

Babban jami'in hukumar kula da tashohin jiragen sama na kasa baki daya, Mista Saleh Dunoma, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawarsa da manema labarai na kafar dillancin labarai ta kasa a garin Abuja.

A jiya Litinin, Mista Dunoma ya bayyana cewa, a halin yanzu duk wata cancanta ta fara gudanar da aikace-aikace a sabuwar tashar ta kammala yayin da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin, watau China Civil Engineering and Construction Company CCECC, ya hadidiye kwangilar wannan aiki cikin gaggawa.

Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama a garin Abuja

Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama a garin Abuja
Source: Depositphotos

Kamar yadda Ministan jiragen sama Hadi Sirika ya kayyade, shugaba Buhari zai halarci bikin kaddamar da sabuwar tashar a ranar 20 ga watan Dasumba da ta yi daidai da ranar Alhamis.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaba Buhari ya gudanar da makamancin wannan lamari yayin da ya kaddamar da sabuwar tashar jiragen sama ta kasa da kasa cikin birnin Fatakwal a watan Oktoba da ya gabata.

KARANTA KUMA: Dalilan Peter Obi yayin muhawara sun yi daidai da bukatun 'Yan Najeriya - Tambuwal

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, gwamnatin shugaba Buhari na ci gaba da ribatar bashin dalar Amurka miliyan 500 da ta karba a hannun bankin China-Exim wajen gudanar da wannan muhimman aikace-aikace a tashoshin jiragen sama na Legas, Fatakwal, Abuja da kuma Kano.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau Talata, shugaban kasa Buhari ya shilla jamhuriyyar Nijar domin halartar bikin tunawa da ranar kafa kasar kafin ta samun 'yancin kai a shekarar a 1960.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel