Tsoro Jonathan ya ji ya mika mulki, kuma Buhari zai iya yin taurin kai idan ya sha kasa a 2019 - Falana

Tsoro Jonathan ya ji ya mika mulki, kuma Buhari zai iya yin taurin kai idan ya sha kasa a 2019 - Falana

Babban Lauyan nan da ke kare hakkin Bil Adama a Najeriya, Femi Falana ya fadi dalilin da ya sa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bar karagar mulki bayan ya Buhari ya tika sa da kasa a 2015.

Tsoro Jonathan ya ji ya mika mulki kuma, kuma Buhari zai iya yin taurin kai idan ya sha kasa a 2019 - Falana

Falana yace ICC ce ta sa Jonathan ya sauka daga karagar mulki
Source: Depositphotos

Femi Falana (SAN) yace Shugaba Goodluck Jonathan ya mikawa Muhammadu Buhari mulki ne saboda gargadin da babban Kotun ICC na Duniya yayi na cewa za a hukunta duk wanda ya tada rikici a Najeriya bayan babban zaben na 2015.

Falana yace wannan jan-kunne da ICC tayi ne ya sa Goodluck Jonathan ya mika mulki a hannun Shugaba Buhari tun da girma da arziki. Babban Lauya Falana yayi wannan jawabi ne a wajen wani taron Lauyoyi da aka yi a Garin Legas.

KU KARANTA: An fadawa Jami'an tsaro su sa ido kan wani Sanata a 2019

Fitaccen Lauyan mai kare hakkin al’umma yake cewa a tarihin Najeriya, Janar Ibrahim Babangida ne kurum ya taba soke zabe a lokacin mulkin Soji, Lauyan yace a halin yanzu babu Shugaban da zai iya yin haka a Najeriya kuma ya sha.

Falana yake cewa da Jonathan yayi gigin kin mika mulki, da Kotun ICC tayi masa irin abin da ya faru da Shugaba Laurent Gbagbo na Kasar Cote d’Ivoire. Lauyan yace yana gani kamar Buhari ba zai bada mulki idan ya fadi zaben 2019 ba.

Jiya Shugaba Buhari yayi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ba duk 'yan takaran 2019 dama domin gwada farinjininsu ba tare da tsangwama ko muzgunawa ba kamar yadda PDP ta rika yi masa a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel