Kyan tafiya: Ronaldo zai koma Madrid

Kyan tafiya: Ronaldo zai koma Madrid

Cristiano Ronaldo, tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zai sake komawa garin Madrid dake kasar Spain domin taka leda a filin wasan kungiyar Atletico Madrid a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai.

A yau, Litinin, ne aka sake fitar da jadawalin karawa a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa 16 da suka fafata a gasar cin kofin zakarun Turai.

A rukunin wasannin da aka fita, kungiyar Juventus da Ronaldo ke bugawa wasa zata kara da kungiyar Atletico a ranar 19 ga watan Fabrairu a filin wasanta da ake kira Metropolitano.

Kungiyar ta Juventus ta bayyana cewar zata isa kasar Spain a ranar 18 ga wata domin samun damar hutawa da yin atisaye domin samun damar fuskantar wasan da zasu buga washegari cikin natsuwa.

Kyan tafiya: Ronaldo zai koma Madrid
Ronaldo
Asali: Getty Images

Hakan zai bawa Ronaldo damar sake taka leda a garin Madrid a karo na farko tun bayan da ya bar kungiyar Real Madrid.

DUBA WANNAN: Gasar zakarun Turai: CSKA ta lallasa Madrid har gida

Kungiyar Juventus ta kammala zagaye na farko a mataki na daya da ywan maki 12 a rukuni na 8, yayinda kungiyar Atletico ta kammala a mataki na biyu da yawan maki 13 a rukuni na farko.

Ronaldo, tsohon dan wasan kwallon duniya sau 4, ya daga kofin gasar zakarun Turai sau 4 tare da kungiyar Real Madrid, sannan shine dan wasan da yafi kowanne yawan zura kwallo a gasar da adadin kwallo 121.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel