Cin hanci ya samu karin matsayi a gwamnatin Buhari - Atiku

Cin hanci ya samu karin matsayi a gwamnatin Buhari - Atiku

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya yi matukar mamakin ganin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, a fadar shugaban kasa bayan an sallame shi daga aiki bisa zargin cin hanci da rashawa.

A cewar Atiku, Babachir ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben Buhari da kungiyar masu goyon Buhari (BSO) ta shirya.

A jawabin da Atiku ya fitar, ya ce "abun takaici ne a ce shugaban kasa ya karrama mutumin da aka kora daga aiki bayan samun sa da laifin cin hanci.

"Faruwar irin wadannan abubuwa ne ya saka hukumar sa-ido a kan cin hanci ta kasa da kasa ta bayyana Najeriya a sahun gaba na kasashen da cin hanci ke kara samun gindin zama," a cewar Atiku.

Cin hanci ya samu karin matsayi a gwamnatin Buhari - Atiku

Atiku
Source: Facebook

A cikin jawabin na Atiku, ya ce idan ba gwamnatin Buhari bata daurewa cin hanci gindi ba, ta amsa masa jerin wadansu tambayoyi kamar haka;

"Wanene ya sake dawo da Maina tare da kara masa matsayi har sau biyu a lokaci daya? "Wanane ya mallaki babban gidan Ikoyi da kudinsa ya kai $42m?

"Me aka yiwa mai tsaron Aisha Buhari wanda ya yi babakere da N2.5bn?

"Me ya sa ba yi bincike kan kwantiragin da kamfanin NNPC ya bayar na $25bn ba tare da ka'ida ba?

"Me ya sa har yanzu ba a kori wadanda suke da hannu a kutsen Buhari na kasafin kudi ba ko kuma aka gurfanar da su gaban kotu?

DUBA WANNAN: Zan basu damar da suka hana ni - Buhari ya yiwa PDP albishir

"Yaushe ne za a gurfanar da Babachir gaban kotu?

"Me yasa kudin tallafin mai ya linka duk da cewar farashin man ya linka shima?

"Me yasa shugaban kasa Buhari ya janye dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar NHIS, Usman Yusuf, kafin matsin lambar jama'a ya tursasashi dakatar da shi? Me ya sa har yanzu ba a kaishi kotu ba?

"A watan Mayu, kungiyar bin diddigi don tabbatar da adalci ta kasa da kasa tayi gargadi cewar Buhari ya kara kudaden da ake warewa tsaro da kashi 600%, sai dai har yanzu sojoji basu da makamai kuma 'yan ta'adda na ci gaba da kashe su. Shin ina kudaden suke shiga ne?

"A watan Fabreru, Buhari ya cire $1bn daga asusun rarar danyen mai don yaki da ta'addanci, sai dai shugaban hafsan sojin kasa, ya ce sojoji basu da makamai, jim kadan bayan harin Metele."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel