Kaso 25% kacal na mijinki ki ka mallaka, kaso 75% na wasu matan ne - Ustaz ya bawa mata shawara

Kaso 25% kacal na mijinki ki ka mallaka, kaso 75% na wasu matan ne - Ustaz ya bawa mata shawara

Fitaccen malamin addinin Islama, Ustaz Abdulfatah Adeyemi, ya yi kira ga mata da su bar wasu matan su mori mazajensu saboda sun mallaki kaso 25% ne na mazajen, yayin da wasu matan suka mallaki kaso 75% na mazajen nasu.

Adeyemi ya fadi hakan ne a Abuja yayin gabatar da wata takardar mai taken "sadaqa, hanyar shiga aljannah" a wani taron kungiyar mata musulmi dake tattara sadaqa domin taimakon mabukata.

Malamin ya kara da cewar duk matan dake kange mazajensu daga kara yin aure "'yan fashi" dake son tattare komai ga kansu.

Ya shawarci mata da su daina hana mazajensu kara aure tare da basu shawarar su kasance masu addu'a ga mazajensu don su kasance masu adalci ga dukkan matan da suka aura.

Kaso 25% kacal na mijinki ki ka mallaka, kaso 75% na wasu matan ne - Ustaz ya bawa mata shawara

Ustaz Abdulfatah Adeyemi
Source: Facebook

Ustaz Adeyemi ya ce halin wasu mata na son mallakar maza ke sanya maza da yawa shiga neman mata.

A cewar sa, "bari na fada maku, mazajenku ba mallakar ku bane; kun mallaki kaso 25% ne kawai, ragowar kaso 75% na wasu matan ne.

DUBA WANNAN: Duk kanzon kurege ne, bani da niyyar barin PDP - Kwankwaso

"Duk mai son ta mallaki mijinta 100% bisa 100% to barauniya ce saboda tana son ta mallaki fiye da kaso 25% da yake nata.

"Ku daina tunanin cewar don namiji ya aure ku wasu matan ba zasu more shi ba.

"Maza ba wawaye bane, kara ma wayo suke yi. Yanzu sai maza sun mutu ake sanin hakikanin adadin 'ya'yansu.

"Ba wai hakan na faruwa ga duk maza bane, amma ina son ku sani maza sun fi ku wayo. Ku ba maza bane, a saboda haka ba zaku san me ke faruwa a zuciyar namiji ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel