'Yan sanda sun kashe maigari da dansa yayin musayar wuta a Sokoto

'Yan sanda sun kashe maigari da dansa yayin musayar wuta a Sokoto

Jam'ian rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto sun hallaka maigarin kauyen gidan Bunu, Alhaji Adduwa, tare da dansa, Aliyu Abdullahi, yayin musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron.

Kazalika rundunar ta sanar da kama mutane 5 da suka dade suna addabar sassan jihar da satar mutane da fashi da makami.

Yayin gabatar da gawar mutanen biyu ga manema labarai, DSP Cordelia Nwawe, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, ta ce ta, "An kama Aliyu Abdullahi ne a kauyen Gawon Fulani yayin da yake tafiya rataye da bindiga a kan babur dinsa. Shi kuma mahaifinsa shine me sayar da makamai ga 'yan ta'addar da suka addabi yankin karamar hukumar Rabah da kauyensu yake.

"Lokacin da ya fuskanci jami'an tsaro na tunkarar gidansa sai ya fara harbi, lamarin da ya saka jami'anmu mayar da martani domin hana shi guduwa. Ya mutu ne bayan an kai shi asibiti domin ceto ransa."

'Yan sanda sun kashe maigari da dansa yayin musayar wuta a Sokoto
'Yan sanda
Asali: Twitter

Ragowar 'yan ta'addar da aka yi bajakolinsu su ne, Abdullahi Isa, Musa Namallam Lawali, Muhammad Lawali, Muhammadu Sani, Ibrahim Alhaji Shu'aibu, Alhaji Haruna Tursa, Ibrahim Garba, Bello Alhaji Danbaba, Umar Maude da Muhammadu Rabiu.

A wani labarin na Legit.ng mai kama da wannan, kun ji cewar rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen jihar Katsina, ta sanar da samun nasarar damke wata tawagar 'yan fashi da makami ta mutane biyar da suka dade suna addabar garuruwan Jihar Katsina da kewaye.

DUBA WANNAN: An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

Jam'ian rundunar 'yan sandan sun yi nasarar cafke 'yan fashin ne a jiya, Juma'a, bayan aikata wani fashi a garin Funtuwa.

Isa Gambo, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, ya bayyana cewar alhaki ne ya kama 'yan fashin bayan sun aikata fashi a gidan wani mutum mai suna Haruna Idris dake unguwar Dan-Dutse a garin Funtuwa.

Gambo ya lissafa sunayen 'yan fashin kamar haka: Umar Yahaya (shekaru 24), Abdulmalik Yahaya (shekaru 20), Abdulrashid Musa (shekaru 20), Abdurrahaman Suleiman da (shekaru 21), dukkansu mazauna kauyen Maigamji dake karkashin karamar hukumar Funtuwa.

Ya kara da cewar an yi nasarar samun makamai da suka hada da bindiga, bindigar wasan yara daya, wukake masu kaifi guda biyu, adda, cocilan, dubu tara da naira tamanin, da wayoyin hannu 4, da kuma hular soji guda daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel