Sojojin Metele: ‘Dan takarar PDP, Atiku yayi kaca-kaca da Buhari da Osinbajo

Sojojin Metele: ‘Dan takarar PDP, Atiku yayi kaca-kaca da Buhari da Osinbajo

- Kwanan nan ne aka bizne Sojojin da aka kashe a Garin Metele

- Shugaba Buhari bai aika ko da wakili zuwa wajen jana’izar ba

- Atiku yace wannan ba karamin abin kunya bane ga Najeriya

Sojojin Metele: ‘Dan takarar PDP Atiku yayi kaca-kaca da Buhari da Osinbajo

Atiku ya nemi Buhari yayi koyi da Shugaban Kasar Faransa Macron
Source: Twitter

‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019, Alhaji Atiku Abubakar, yayi tir da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, na kin halartar bizne wasu Sojojin Najeriya.

Atiku Abubakar ya koka game da yadda Shugaban kasa da Mataimakin sa su ka ki zuwa wajen jana’izar Sojojin Najeriya da aka kashe a Garin Metele a Jihar Borno kwanaki. Atiku yace wannan abu da da Gwamnati tayi bai dace ba.

KU KARANTA: 'Yan ta'adda cikin kayan 'yan agaji sun kashe Sojan Najeriya

‘Dan takarar Shugaban kasa na babban Jam’iyyar hamayya ta PDP ya fitar da wannan jawabi ne a Ranar Asabar, inda yace babbun abin takaicin shi ne yadda Shugaban kasar ya gaza tura ko da wakili wajen taron jana’izar Sojojin Kasar.

Atiku ya nemi Shugaba Buhari yayi koyi da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, wanda ya fasa zuwa ofis a farkon shekarar nan bayan ‘Yan ta’dda su kashe wani babban Sojan Faransa mai suna Laftana Kanal Arnaud Beltrame.

Alhaji Atiku Abubakar yace idan har Shugaban kasa Buhari ya na da lokacin da zai gana da ‘Yan wasan kwaikwayo, babu dalilin da zai sa ba zai iya halartar jana’izar bizne Sojojin Najeriya da su ka mutu a hannun ‘Yan ta'addan Boko Haram ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel