2019: APC ba za tayi facaka da kudi wajen yakin neman zabe ba

2019: APC ba za tayi facaka da kudi wajen yakin neman zabe ba

Mun fara samun kishin-kishin din cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna cewa ba zai kashe makudan kudi wajen yakin neman zaben 2019 ba saboda halin da tattalin arzikin Kasar nan yake ciki.

2019: APC ba za tayi facaka da kudi wajen yakin neman zabe ba
Buhari zai kafa tarihi wajen yakin zabe na rashin barnar kudi
Asali: Depositphotos

The Nation ta rahoto cewa Shugaban kasa Buhari ya haramtawa Hukumomin Gwamnatin Tarayya bada gudumuwar kudi domin shiryawa yakin neman zaben Jam’iyyar APC a 2019. Shugaban kasar bai da niyyar kashe kudi sosai a zaben.

Yunkurin gujewa kashe kudi ne ya sa Shugaba Buhari ya ki rantsar da kwamitin yakin neman zaben Shugaban kasa watau PCC. Halin da tattalin arzikin Kasar ya shiga ya sa Buhari bai so a kashe kudi sosai wajen kamfen a 2019.

KU KARANTA: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - Inji INEC

Dokar zabe dai ta bada dama ne a kashe Naira Biliyan 1 rak wajen yakin neman zaben Shugaban Kasa. Haka kuma masu neman takarar Gwamna za su iya kashe Naira Miliyan 200, yayin da ‘Yan Majalisa ke kashe kasa da Miliyan 40.

A jiya da dare ne Shugaban kasar ya kaddamar da kwamitin neman takarar sa na zaben 2019. Shugaba Buhari yana da niyyar yin kamfen din wata guda ne kurum domin ganin ba ayi asarar kudin Gwamnati wajen yakin zabe ba.

Wannan ne dai karon farko da Shugaban Kasa ba zai kashe kudi sosai wajen yakin neman zabe ba. A baya Gwamnatin PDP ta rika kada watsi da kudin Kasa wajen yin kamfe a zabukan da aka rika yi a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel