Dalilan Peter Obi yayin muhawara sun yi daidai da bukatun 'Yan Najeriya - Tambuwal
Ko shakka ba bu a makon da ya gabata aka gudanar da muhawara a tsakanin wasu 'yan takara biyar da ke hankoron kujerar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019, inda suka baje dalilai da kudirori na salon gudanar da shugabanci.
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana kyakkyawan ra'ayi na goyon bayan dan takara na jam'iyyar PDP, Peter Obi, dangane da sakamakon muhawarar da ta gudana a ranar Juma'ar da ta gabata.
Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa, muhawarar ta fayyace yadda 'yan Najeriya ke da babbar bukata ta samun mataimakin shugaban kasa mai nagarta makamanciyar ta Peter Obi, da ya kasance abokin tafiya na dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Tsohon kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa, kudorori gami da salon gudanar da shugabanci na dan takarar jam'iyyar PDP sun yi daidai da bukatu na tunkarar matsalolin da al'ummar kasar nan ke fuskanta tare da magance su cikin kankanin lokaci.
Jaridar Legit.ng ta ruwaiito cewa, an gudanar da muhawar tsakanin 'yan takara biyar da suka hadar da Farfesa Yemi Osinbajo (APC), Peter Obi (PDP), Umma Getso (YPP), Alhaji Abdulganiyu Galadima (ACPN), da kuma Khadija Abdullahi Iya (ANN).
KARANTA KUMA: Makaryatan 'Yan Jarida sun ruwaito daga kasar Mali na fito - El-Rufa'i
Tambuwal ya kara da cewa, ko shakka ba bu kudorin Obi sun tabbatar da cikakkiyar fahimtar sa habaka tattalin arzikin kasar nan tare da inganta jin dadi al'ummar kasar nan.
A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Shehin Malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Shu'aibu, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dan takarar shugaban na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, akan kauracewa cin mutuncin juna.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng