Jerin Jihohin Najeriya da ba su da wakilici a Majalisar FEC

Jerin Jihohin Najeriya da ba su da wakilici a Majalisar FEC

Yanzu haka akwai Jihohin da ba su da Minista a Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a sakamakon murabus da Ministocin su kayi ko kuma samun wani mukami dabam. Legit Hausa ta kawo jerin wadannan Jihohi.

Jerin Jihohin Najeriya da ba su da wakilici a Majalisar FEC

Ministan ma’adanan Najeriya ya zama Gwamnan Jihar Ekiti
Source: Depositphotos

1. Jihar Ekiti

Kawo yanzu Jihar Ekiti ba ta da wakilci a Majalisar zartarwa ta Tarayya. An samu hakan ne bayan Dr. Kayode Fayemi ya lashe zaben Gwamnan Jihar ta Ekiti a Jam’iyyar APC mai mulki watanni baya da su ka wuce.

KU KARANTA: Ba a taba Shugaban kasa mai irin tsantsar gaskiya Buhari ba - Shehu Sani

2. Jihar Ogun

A Watan Satumba ne kuma Kemi Adeosun ta ajiye mukamin ta na Ministar kudi saboda zargin amfani da takardun bogi. Kamar tsohon Ministar Ma’adanai Fayemi, Ita ma Adeosun ta fito ne daga Jihar Ekiti a Kasar Yarbawa.

3. Jihar Nasarawa

A makon nan ne kuma Jihar Nasarawa ta rasa wakilci a Majalisar Ministoci bayan da Ibrahim Jibril yayi murabus bayan ya samu sarautar Kasar Nasarawa. Ministan muhallin zai ajiye siyasa ne domin ya fuskanci rikon kasar sa.

A baya dai an samu wadanda su ka bar kujerar su a Gwamnatin Shugaba Buhari. Daga ciki akwai Aisha Mohammed wanda ta samu babban aiki a Majalisar dinkin Duniya da kuma irin su James Ocholi wanda ya rasu a hadarin mota.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel