Yemi Osinbajo yace aikin Mataimakin Shugaban kasa sam ba wasa bane

Yemi Osinbajo yace aikin Mataimakin Shugaban kasa sam ba wasa bane

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yayi karin haske game da matsayin sa na Mataimakin na Shugaba Muhammadu Buhari. Osinbajo yace kundin tsarin mulkin kasa ya fayyace aikin sa.

Yemi Osinbajo yace aikin Mataimakin Shugaban kasa sam ba wasa bane
Aikin wanda ke rike da mukamin Mataimakin Shugaban kasa da yawa inji Osinbajo
Asali: Facebook

Yemi Osinbajo yayi wannan jawabi ne a lokacin da su ke tafka muhawara da sauran ‘Yan takarar Mataimakin Shugaban kasa da Hukumar NEDG da BON su ka shirya a shekaran jiya. Osinbajo ya kara da sauran Abokan hamayyar sa.

Osinbajo yace aikin da ke kan Mataimakin Shugaban kasa ba karamin aiki bane, sai dai duk da haka, Osinbajo yace akwai riba a hidimar da yake yi wa Kasar sa. Osinbajo yace yawan ayyukan da ke gaban sa ne ya sa duk ya tsufa tukuf.

Farfesa Yemi Osinbajo yake cewa a lokacin da ya soma aiki da Shugaba Buhari a tsakiyar 2015, babu furfura sosai a kan sa, amma yanzu furfurar ta cika gashin sa. Osinbajo yace shi ne babban mai ba Shugaban kasa Buhari shawara a ofis.

KU KARANTA: Duk abin da ya fada hannun Atiku ba ya taba lalacewa - Inji Dogara

Mataimakin Shugaban Kasar yace duk lokacin da Shugaban kasa ba ya nan, shi ne yake tsaya masa. Haka kuma tsarin mulki ta ba Mataimakin Shugaban kasa dama ya jagorancin ragamar wasu manyan Hukumomi 22 da ake da su a Najeriya.

Farfesa Osinbajo yake cewa aikin sa bai tsaya a nan ba kurum, domin kuwa shi ne Shugaban Majalisar da ke mallakawa ‘Yan kan kasuwa da masu jari kadarorin Gwamnati a matsain gwanjo. Osinbajo yace aikin na sa kuma yana bukatar hakuri.

Mataimakin Shugaban kasar na Najeriya, Osinbajo yace ba ko yaushe yake yin na’am da tsare-tsaren Gwamnati ba don haka wani abin dole sai yayi hakuri matuka. Osinbajo yace duk da haka ya wuce ace masa saniyar ware a Gwamnatin Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel