Duk abinda aka damka a hannun Atiku, ba ya taba lalacewa - Dogara

Duk abinda aka damka a hannun Atiku, ba ya taba lalacewa - Dogara

Kakakin majalisar wakilai na Najeriya, Honarabul Yakubu Dogara ya ce duk abinda aka damka a hannun dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar baya taba lalacewa.

The Cable ta ruwaito cewa Dogara ya yi wannan furucin ne a ranar Asabar wajen walimar daurin auren dan uwansa Hassan Ishaya da amaryarsa Mafeng a babban birnin tarayya, Abuja.

Kakakin majalisar ya ce Abubakar ne dan takarar da zai fitar da Najeriya daga kangin talauci da ya yi mata katutu.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya su zabi mutumin da ya samu kwarewa da horaswa da zai iya kawo gyara a kasar.

Duk abinda aka damka a hannun Atiku, ba ya taba lalacewa - Dogara

Duk abinda aka damka a hannun Atiku, ba ya taba lalacewa - Dogara
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

"Idan ka dubi Wazirin Adamawa a matsayin shugaba a Najeriya, kuma ka sake bincikawa a duk lunguna da sakon Najeriya ba za ka taba iya kidaya mutanen da Atiku ya gina ba.

"Sirrin shine duk abinda ke sanya a hannun Waziri, abun baya tabarbarewa. Idan ka saka ilimi a hanunsa, zai zama jami'a. Shine ya kafa daya daga cikin jami'an mafi inganci a Najeriya. Idan ka saka kudi a hannunsa, ba zai tabarbare ba.

"Wadanda ke kishin cewa duk abinda ka saka a hannunsu yana tabarbarewa za su ta kokarin sukar sa amma maganar gaskiya shine da wahala ka saka abu a hannun Atiku abin ya lalace.

"Saboda haka idan muna da wayyo a kasar nan yanzu da abubuwa da dama ke tabarbarewa, kamata ya yi mu damka kasar a hannunsa. Ina fada maka idan muka saka tattalin arzikin Najeriya a hannunsa, kowa na iya zuwa ya yi barci, za ku ga abinda zai faru," inji Dogara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel