Limamai ke kara daurewa cin hanci gindi - shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali

Limamai ke kara daurewa cin hanci gindi - shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali

Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, ya zargi malaman addini, da suka hada da limamai, da daurewa cin hanci gindi ta hanyar kin kushe mabiyansu dake aikata laifin cin hanci.

Hameed Ali na wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman Abuja da aka yi yau, Asabar.

Shugaban na hukumar kwastam na daga cikin manyan bakin da limaman suka gayyatar domin su gabatar da jawabi.

Hameed Ali ya shaidawa limaman cewar suna da gudunmawar da zasu bayar wajen dakile cin hanci da rashawa a tsakanin al'ummar Najeriya.

Limamai ke kara daurewa cin hanci gindi - shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali
Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali
Asali: Original

A nasa jawabin, malami mai gabatar da jawabi, Farfesa Auwalu Yadudu na jami'ar Bayero dake Kano, ya bukaci limaman su samu hanyoyin shigowar kudi a kan dogaro da sadaka ko tallafi.

Yadudu, wanda Sheikh Tajuddeen Bello, ya wakilta, ya ce yin hakan zai bawa malaman kariya daga goyon bayan duk wani abu mai alaka da cin hanci.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar shugaban hukumar kwastam ta kasa (NCS), Hameed Ali, ya ce zai kori dukkan jami'in kwastam da ya fadi jarrabawar kwalejin hukumar sau uku.

Shugaban na wannan kalami ne a wurin bikin yaye manya da kananan jami'an hukumar kwastam da suka kammala karatu a kwalejin kwastam ta Abuja a jiya, Juma'a.

Ya bayyana cewar yin hakan na daga cikin sabbin dokokin hukumar kwastam na inganta aiyukan jami'anta.

Kazalika ya bayyana cewar halartar kwalejin horon ya zama dole ga kowanne jami'in hukumar daga yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel