Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

Gabanin babban zaben shekarar 2019, a kalla 50% na 'yan majalisun wakilai 360 ma su ci a yanzu ba za su koma majalisar ba a sabuwar shekarar.

Wani bita da Premium Times ya yi ya nuna cewa mafi yawancin 'yan majalisar sun fadi zabukkan cikin gida yayin da wasu kuma suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun domin yin takarar wasu kujerun.

Ga dai jerin 'yan majalisar wakilai da tabbas ba za su koma majalisa ba.

1. Abia

Nnenna Elendu-Ukeje (PDP), 'yar majalisar mai wakiltar mazabar Bende ba za ta koma majalisa ba saboda ta fadi zaben cikin gida, kuma ba ta sauya sheka zuwa wata jam'iyya ba domin tayi takarar.

2. Adamawa

Shuaibu Abdulrahman, Abubakar Lawal da Adamu Kamale, mutum uku cikin 'yan majalisu takwas daga jihar Adamawa ba za su koma majalisa ba. Shuaibu Abdulrahman, Abubakar Lawal sun fadi zaben cikin gida shi kuma Adamu Kamale ya yi takarar kujerar Sanata ya fadi.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

3. Akwa Ibom

Emmanuel Ikon and Owoidighe Ekpoatai, 'yan majalisa biyu cikin 10 daga jihar Akwa Ibom ba za su koma ba saboda sun sha kaye a zaben cikin gida.

4. Bauchi

Shehu Aliyu da Adamu Gurai, 'yan majalisun biyu sun sha kaye tun a zaben fidda gwani hakan ya sa ba za su samu damar komawa majalisar.

5. Bayelsa

Sodagumo Omoni (PDP), Kamar wasu da yawa a jerin 'yan majalisar, Omoni ya sha kaye a zaben cikin gida shi yasa ba zai koma majalisa ba/

6. Benue

Dickson Tackighir, Saleh Hassan, Emmanuel Udende and Ezekiel Adaji, wadannan 'yan majalisar hudu duk sun sha kaye a zaben cikin gida.

7. Borno

Asabe Vilita, Muhammed Sheriff and Ayuba Bello, Dukkansu sun gaza samun tikin takara a jam'iyyarsu.

8. Delta

Onyemaecho Mrakpor, Idisi Lovette and Daniel Reyanju, suma sun sha kaye ne a zaben fidda gwani hakan yasa ba za su koma majalisar ba.

9. Ebonyi

Linus Okorie, mai wakiltar mazabar Ivo/Ohaozara/Onicha ba zai koma majalisa ba saboda ya fadi zaben cikin gida.

10. Edo

Pally Iriase, ba zai koma majalisa ba saboda tsarin karba-karba da ake yi a mazabarsa.

11. Ekiti

Olamide Johnson, mai wakilatar Ijero/Ekiti West/Efon shima ya sha kaye a zaben fidda gwani.

12. Enugu

Kamar yadda ta ke a jihar Ekiti, dan majalisa daya ne ba zai koma ba a jihar Enugu, Chukwuemeka Ujam mai wakiltan Nkanu ta Gabas/Kudu ya sha kaye a zaben fidda gwani.

13. Abuja

'Yan majalisa biyu ne daga Abuja suka ci taliyar karshe, Zephaniah Jisalo da Zakari Angulu duk sun fafata a zaben cikin gida amma har yanzu ba a tsayar da wanda zai kara da Philip Aduda na PDP ba.

14. Gombe

Biyu cikin 'yan majalisa na jihar Gombe ba za su koma ba. A yayin da Binta Bello da samu tikitin Gombe na Kudu, Samaila kashena ta sha kaye a zaben fidda gwani.

15. Imo

Chukwukere Austin da Goodluck Opiah suma ba za su koma majalisa ba saboda sun fadi zaben fidda gwani.

16. Jigawa

A jihar Jigawa, 'yan majalisa uku ba za su koma ba saboda sun gaza samun tikitin takara a jam'iyyunsu. 'Yan majalisar sune Sani Zorro, Rabiu Kaugama da Muhammad Boyi.

17. Kaduna

Jihar Kaduna itace tafi yawan 'yan majalisar da ba za su koma ba. 'Yan majalisa 7 ne suka ci taliyar karshe a jihar Kaduna, sune Adams Jagaba, Muhammad Soba, Sunday Marshal, Muhammed Abubakar, Yusuf Bala, Mohammed Usman da Lawal Rabiu.

Sauran sun sha kaye ne zaben cikin gida amma Mr Marshal ya tafi takara ne a matsayin mataimakin gwamna a PDP a zaben 2019.

18. Kano

Wadanda ba za su koma a Kano ba sune Aliyu Madaki, Bashir Baballe, Nasiru Baballe da Mukhtar Chiromawa.

19. Katsina

Mutum daya ne kawai ya sha kaye a zaben fidda gwani a Katsina, Aliyu Sani.

20. Kogi

Sunday Karimi na jam'iyyar PDP ba zai koma ba saboda ya sha kaye a hannun Dino Melaye.

21. Kwara

'Yan majalisa uku ba za su koma ba a jihar Kwara, sun hada da Razak Atunwa, Zakari Mohammed da Amuda Kanike.

22. Lagos

'Yan majalisa shida ne daga Legas suka yi bankwana da majalisar, 'yan majalisar sune Tony Nwulu, Adaranijo Abiodun, Joseph Adebayo, Bamgbose Joseph da Diya Babafemi.

23. Nasarawa

Bisa ga dukkan alamu 'yan majalisa uku daga jihar Nasarawa ba za su koma ba, 'yan majalisar sune David Ombugadu, Mohammed Onawo da Jaafar Ibrahim.

24. Niger

'Yan majalisar da suka gaza samun tikitin takara a jihar Neja sune Adamu Chika, Faruk Mihammadu da Saleh Shehu.

25. Ogun

A jihar Ogun kuma Olusegun Williams da Kehinde Olusegun ne suka sha kaye a zabukkan fidda gwani.

26. Ondo

Kamar jihar Ogun, su ma a jihar Ondo mutum uku ne suka ci taliyar karshe, Babatunde Kolawole, Baderinwa Samson and Akinfolarin Mayowa.

27. Osun

A jihar Osun, Yusuf Lasun ne ba zai koma majalisa ba saboda ya saki kujerarsa ya yi takarar gwamna amma ya sha kaye hannun Gboyega Isyaka.

28. Oyo

'Yan majalisa biyu ne ba za su koma ba saboda sun fadi zaben cikin gida, sune Ayoade Ojoawo and Oladele George.

29. Plateau

Edward Pwajok da Istifanus Gyang ne ba za su koma ba saboda sun sha kaye a zabbukan cikin gida.

30. Rivers

Chidi Frank ya sha kaye a zaben cikin gida yayin da Betty Apiafi ta tafi takarar Sanata.

31. Taraba

Mutum daya ne kawai ba zai koma ba saboda ya fadi zaben cikin gida, Mr Malle Ibrahim mai wakiltan alingo/Yorro/Zing.

32. Yobe

A jihar Yobe ma, Ismaila Gadaka ne kadai ya rasa tikitin sake takara.

33. Zamfara

A jihar Zamfara dukkan 'yan takarar APC ba za su koma ba saboda rashin bayar da sunayen 'yan takara a kan lokacin da jam'iyyar ba tayi ba yasa INEC ta rufe wa'addin karbar sunayen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel