'Yan ta'adda sun kashe tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matar sa

'Yan ta'adda sun kashe tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matar sa

- Wasu 'yan daba sun kashe tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matarsa a jihar Imo

- Tsohon kwamishinan ya koma kauyensu ne bayan ya yi murabus daga aiki domin ya fara kasuwanci

- 'Yan daban sun haura katangar gidansa cikin dare ne suka kashe shi da matarsa kuma suka sulale har yanzu ba a gano su ba

Al'ummar garin Umuoke Obowo a karamar hukumar Obowo na jihar Imo sun tashi cikin bakin ciki sakamkon kisar gillar da aka yiwa tsohon kwamishinan 'yan sanda mai murabus, Innocent Brown da matarsa.

Punch ta ruwaito cewar wasu bata gari da ba gano ko su wanene ba suka kashe tsohon kwamishinan da matarsa a kauyensu a ranar Juma'a.

'Yan ta'adda sun kashe tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matar sa

'Yan ta'adda sun kashe tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda da matar sa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

A cewar majiyar, 'yan ta'addan sun haura katangar gidan tsohon kwamishinan ne kuma suka kashe shi da matarsa yayin da suke barci.

Daya daga cikin wanda suka bayar da shaida a kan lamarin ya ce, "Innocent Brown tsohon kwamshinan 'yan sanda ne da ya yi murabus, ya dawo kauye ne domin ya fara kasuwanci.

"Mummunar lamarin ya afku ne a daren Alhamis inda aka kashe shi tare da matarsa.

"Wasu 'yan daba da ba gano ko su wanene ba suka haura katangar gidansa suka kashe shi da matarsa.

"Ihunsu ne ya sanya muka farka daga barci. Kafin a kai musu dauki har sun mutu. Wadanda suka aikata kisar sun gudu kuma har yanzu ba a gano ko su wanene ba."

Majiyar Legit.ng ya gano cewar an ajiye gawan tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sandan da matarsa a dakin ajiye gawa na asibitin Obowo.

A yayin da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Orlando Ikokwu ya ce har yanzu bai samu cikaken bayani a kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel