Dabi'u 4 da kan iya taba lafiyar ido ko haddasa makanta

Dabi'u 4 da kan iya taba lafiyar ido ko haddasa makanta

Ido na daga cikin halittun jikin mutum masu matukar muhimmanci. Da idanu ne mutane da dabbobi kan iya gani. Rashin idanu ba kankanuwar tawaya bace ga mutum ko dabba.

Wasu daga cikin mutane ana haifar su ne da matsalar ido, wasu kuwa daga baya suke gamuwa da larura ko cuta dake lalata masu idanu.

Bisa la'akari da muhimmancin ido ne, legit.ng ta kawo maku wasu abubuwa 4 da masana suka ce na taba lafiyar ido ko ma su haddasa makanta.

1. Hatsari yayin motsa jiki: Duk da motsa jiki nada matukar mahimmanci ga lafiyar jiki, a kan gamu da hatsari da kan iya nakasta mutum.

Masana sun shawarci masu sha'awar motsa jiki dasu kula sosai da idanuwansu yayin motsa jiki musamman wasannin masu hatsari da ake amfani da karfi sosai.

Dabi'u 4 da kan iya taba lafiyar ido ko haddasa makanta

Dabi'u 4 da kan iya taba lafiyar ido ko haddasa makanta
Source: Twitter

2. Hasken UV: Hasken Ultraviolet kan iya haifar da makanta, musamman idan mutum na yawan kallonsu ko dadewa a wurin da suke. Suna jawo yanar ido, dajin ido da wasu matsalolin ido masu yawa.

DUBA WANNA: Alamomi 7 da zaku gane koda ta fara samun matsala

3. Tabarau: Babban dalilin amfani da tabarau shine kare idanu daga kura ko tsananin haske. Da yawan jama'a na amfani da tabarau ba tare da sanin wanne iri bane, masana sun gargadi jama'a da suke neman shawarar kwararru kafin fara amfani da tabarau.

4. Tabarau na magani: Wasu nau'ikan tabarau da ake amfani da su domin magance matsalar idanu kan iya lalata ido idan gilashinsu ya karye ya taba idanu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel