Tsaro: Dan sanda ya gina caji ofis kyauta a Zamfara

Tsaro: Dan sanda ya gina caji ofis kyauta a Zamfara

- Wani jami'in dan sanda, Murtala Muhammad Sani, ya bayar da kyautar wani gini ga rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara

- Ya bayyana cewar ya bayar da kyautar ginin ne a matsayin gudunmawar sa a bangaren inganta tsaro a jihar

- Jin dadin wannan kyauta ta DSP Sani ya saka sarkin Gusau, Alhji Ibrahim Bello, yi masa godiya da sa masa albarka

Jami'in rundunar 'yan sanda, Murtala Muhammad Sani; mai mukamin DSP, ya bayar da wani gini kyauta ga hukumar 'yan sanda a jihar Zamfara domin mayar da shi caji ofis.

Kamfanin dillancin labarai na kas (NAN) ya rawaito cewar kwamishinan 'yan sanda a jihar Zamfara, Usman Belel, ya kaddamar da caji ofis din dake unguwar Tsauni, a jiya, Alhamis.

DSP Sani, tsohon dogarin tsohon gwamnan jihar Kogi, Kaftin Idris Wada, ya ce ya bayar da kyautar ginin ne a matsayin gudunmawar sa wajen inganta aiyukan tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara.

Tsaro: Dan sanda ya gina caji ofis kyauta a Zamfara

Shugaban rundunar 'yan sanda; Ibrahim Idris
Source: UGC

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara ya nuna jin dadinsa bisa abinda jami'in dan sandan ya yi.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram: An tabbatar da mutuwar Kaftin Kabiru Hamza

Alhaji Bello Dankande, kwamishinan kananan hukumomi a jihar Zamfara, ya yi godiya ga DSP Sani tare da yin kira ga masu hali a jihar dasu kwaikwayi irin abin kirkin da jami'in dan sandan ya yi.

Kazalika, sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, ya yi godiya ga DSP Sani ta bakin wakilinsa a wurin taron bude sabon ofishin, Alahji Dahiru Shehu; Madawakin Gusau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel