Sayan nagari maida kudi gida: Yan fansho sun bayyana mulkin Buhari a matsayin ‘Gagara tsara’

Sayan nagari maida kudi gida: Yan fansho sun bayyana mulkin Buhari a matsayin ‘Gagara tsara’

Dubun dubatan tsofaffin ma’aikatan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya sun jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa namijin kokarin da yake yi wajen fitar dasu kunya tare da kawar musu da kangin rayuwa ta hanyar biyansu hakkokinsu.

Tsofaffin ma’aikatan da aka fi sani da suna yan fansho sun bayyana haka ne cikin wata wasika da suka aika ma shugaba Buhari da sunan kungiyarsu, Nigerian Unionof Pensioners, Contributory Pension Scheme Sector, NUPCPS, dake dauke da sa hannun shugabanta kwamared Sylva C. Nwaiwu.

KU KARANTA: Shugaban majalisar dattawa ya shiga rudani kan takamaimen adadin Sanatocin Najeriya

Sayan nagari maida kudi gida: Yan fansho sun bayyana mulkin Buhari a matsayin ‘Gagara tsara’

Yan fansho
Source: UGC

Legit.com ta ruwaito kungiyar yan fanshon ta bayyana mulkin Buhari a matsayin wanda tafi taimakonsu tare da darajasu a wajen biyansu hakkokinsu a cikin shekaru goma sha hudu, don haka suke jinjina masa tare da san barka.

Wasikar ta kara da cewa kungiyar ta yanke shawarar aika ma shugaba Buhari takardar jinjina ce bayan taronta data gudanar karo na uku, inda ta samu ganawa da hukumar kula da yan fansho ta kasa, PENCOM a Maitama Abuja.

Kungiyar ta musanta zargin siyasantar da ayyukanta, inda tace “Mun kunshi manyan mutane dattijai wadanda suka bauta ma Najeriya da karfinsu da lafiyansu, kuma mutanene masu fadan gaskiya komai dacinta, don haka babu ruwanmu, zamu fadi gaskiya game da gwamnatinka a ko ina ba tare da shakkar kowa ba.”

Haka zalika kungiyar ta yaba ma Buhari game da matakin daya fara dauka bayan darewarsa madafan iko a shekarar 2015 inda ya saki makudan kudade ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi domin su biya yan fansho hakkokinsu.

Daga karshe kungiyar tayi kira da Buhari ya cigaba da aikin daya fara na sakan ma jihohi kudi suna biyan yan fansho hakkokinsu, domin a cewarsa har yanzu akwai jihohin da yan fansho ke binsu bashin hakkokinsu

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel