Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya kan fahimtar juna da zaman lafiya yayin zaben 2019

Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya kan fahimtar juna da zaman lafiya yayin zaben 2019

A yayin da babban zaben kasa na 2019 ke ci gaba da karatowa, a yau Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi wani muhimmina kira ga al'ummar kasar nan dangane da babban zaben domin kare martabar Najeriya a idon duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma'a, ya gargadi dukkanin al'ummar kasar nan kan dabbaka hudubar hakuri gami da juriya tare hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya yayin da babban zaben kasa na 2019 ke daf da gudana.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne yayin karbar bakuncin wata kungiyar ci gaban al'umma da kuma Matasa ta NNCYD, National Network for Community and Youth Development, yayin da ta ziyarci fadar shugaban kasa bisa jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Yayale Ahmed.

Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya kan fahimtar juna da zaman lafiya yayin zaben 2019

Buhari ya gargadi 'Yan Najeriya kan fahimtar juna da zaman lafiya yayin zaben 2019
Source: Depositphotos

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa, amsa wannan kira ya zamto wajibi kasancewar sa nauyi da rataya a wuyan dukkanin al'ummar kasa baki daya.

Kazalika shugaban kasar ya bayyana cewa, mikewa tsaye kan wannan kira zai yi tasirin gaske wajen dakaci tare da kawar da 'yan siyasa ma su son zuciya da rashin kishin kasa gami da amfani addini da akidar siyasa wajen cimma burikan su.

KARANTA KUMA: 'Yan Jarida 251 na ci gaba da shan dauri a gidajen kaso dake fadin Duniya - CPJ

Shugaban kasar ya kuma yabawa kungiyar ta NNCYD tare da jagoranta dangane da jajircewar su ta tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al'umma mabambanta ra'ayoyi na siyasa da kuma na bambancin akida ta addini a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kotu ta kwace takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Donald Duke, ta kuma danka ta a hannun tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel