Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! An tafka rashin babban Malamin addinin Musulunci

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! An tafka rashin babban Malamin addinin Musulunci

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , Allah yayi ma wani fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Tijjani Khalifa rasuwa a ranar Laraba 12 ga watan Disamba, Shehin Malamin ya shahara a tsakanin mabiya darikar tijjaniya.

Legit.com ta ruwaito Shehin Malamin ya rasu ne bayan wata yar gajeriyar jinya, kuma ya rasu yana da shekaru saba’in da uku, 73, a rayuwa, kuma yam utu ne a garin Zaria ta jahar Kaduna, kamar yadda wani dan uwansa ya tabbatar.

KU KARANTA: Kaiƙayi koma kan mashekiya: Wata yar ƙunar baƙin wake ta kai hari a Borno, ya ƙare akanta

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! An tafka rashin babban Malamin addinin Musulunci
Khalifa
Asali: UGC

Malam Tijjani na daga cikin masu gudanar da kungiyar amintattu ta Munazzamatul Fityanul Islam, inda rahotanni suka tabbatar ya taka rawar gani tare da bada gagarumar gudunmuwa wajen cigaban wannan kungiya.

Daga karshe Malam Tijjani ya rasu ya bar mata hudu, da yaya talatin da biyu, kuma an gabatar da jana’izarsa da misalin karfe 2:30 na ranar Alhamis a babban Masallacin Juma’a na Gwargwaje.

Idan za’a tuna a ranar 25 ga watan Nuwamba ne Allah ya yi ma tsohon gwamnan jahar Kaduna, Birgediya Abba Kyari rasuwa bayan doguwar jinya da yayi fama da ita, kamar yadda muka ruwaito.

Shi dai Abba Kyari ya zama gwamnan Arewa ta tsakiya ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, janar Yakubu Gowon, daga ranar 28 ga watan Mayu zuwa watan Yuli na shekarar 1975.

A shekarar 1967 ne janar Yakubu Gowon ya samar da jihohi goma sha biyu a Najeriya bayan ya rushe shiyyoyin Arewa da na Kudancin Najeriya, inda a cikin shiyya Arewa kadai sai daya samar da jihohi guda shida, daga cikinsu akwai jahar Arewa ta tsakiya, wanda daga bisani aka canja mata suna zuwa Kaduna a shekarar 1976.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng