Za a fara daure Barayin kayan wuta na tsawon shekaru 7 a gidan yari

Za a fara daure Barayin kayan wuta na tsawon shekaru 7 a gidan yari

- Ana neman kafa wani kudiri mai suna “A Bill for an Act to prohibit and prevent electricity theft, power infrastructure vandalism and power company protection 2017”

- Wannan kudiri da ke hannun Sanatocin Najeriya a yanzu zai sa a rika daure barayin kayan wuta har na tsawon shekaru 7 a gidan kurkuku idan har ya zama doka mai cikakken iko

Za a fara daure Barayin kayan wuta na tsawon shekaru 7 a gidan yari
Shugaba Buhari zai haramta satar kayan wutan lantarki a Najeriya
Asali: Facebook

Labarin da mu ke samu shi ne Gwamnatin Tarayya tana neman hanyar kama Barayin kayan wutan lantarki a Najeriya. Wannan ya sa ake kokarin kawo dokar da za ta sa a rika daure wanda aka kama yana satar kayan wuta.

Gwamnatin Tarayya tana yunkurin kawo dokar da za ta haramta satar kayan aikin wuta. Kungiyar NERC mai lura da sha’anin wuta na Kasar ne ke kokarin kawo wannan kudiri ta hannun Shugaban ta watau James Adeche Momoh.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa na yunkurin bankara Shugaba Buhari a kan kudirin zabe

Yanzu dai Farfesa James Adeche Momoh ya mika wannan kudiri da zai yi maganin Barayin kayan wuta a Kasar zuwa gaban Majalisa. Kudirin ya shiga hannun kwamitin da ke lura da sha’anin wutan lantarki a Majalisar Dattawa.

Sanatan PDP na Yankun Abia, Enyinnaya Abaribe, shi ne ke jagorantar wannan kwamiti a Majalisar Dattawa. Ana sa rai kwamitin za yi aikin sa, sannan kuma a kawo kudirin zuwa gaban sauran Sanatocin Kasar domin a tattauna.

Hukumar NERC tana kokarin ganin an fara yankewa masu karkatar da allon wuta ko yin awon gaban da na’urorin wuta da kuma satar kayan aiki irin su wayoyi da taransufoma hukuncin daurin shekara da shekaru 7 a gidan yari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel