Ana kalubalantar nasarar da Tambuwal ya samu a Jam’iyyar APC tun 2014

Ana kalubalantar nasarar da Tambuwal ya samu a Jam’iyyar APC tun 2014

- Wasu ‘Yan APC su na karar nasarar da Tambuwal ya samu a zaben 2014

- ‘Yan takarar sun ce bai dace Jam’iyya ta saida Gwamnan tun a farko ba

- Lauyan APC ya koma bayan ‘Yan takaran bayan Tambuwal ya koma PDP

Ana kalubalantar nasarar da Tambuwal ya samu a Jam’iyyar APC tun 2014
‘Yan APC sun maka Tambuwal kara a gaban babban Kotun Najeriya
Asali: Facebook

Jam’iyyar APC ta shigar da karar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto gaban Kotu inda ta ke nema a sauke Gwamnan daga kujerar sa. APC tace ba a bi matakin da ya dace tun farko wajen tsaida Tambuwal takara ba.

A kwanakin baya Sanata Umar Dahiru da kuma Aliyu Abubakar Sanyinna sun maka Tambuwal a manyan Kotun Kasar inda su ke kalubalantar nasarar da ya samu na lashe zaben fitar da gwani da aka yi a Jam’iyyar APC a 2014.

KU KATANTA: Ba girman Obasanjo ba ne ya rika sukar Buhari - Abdullahi Adamu

Jam’iyyar mai mulki ta juyawa Gwamnan baya ne saboda sauya-sheka da yayi zuwa PDP. Yanzu Abduganiyu Arobo wanda shi ne sabon Lauyan APC a shari’ar da ake yi da Gwamnan ya marawa Dahiru da Sanyinna baya a Kotu.

APC ta dauko hayan sabon Lauyan ne a madadin Jibrin Okutepa wanda a baya ya rika kokarin kare Aminu Tambuwal kafin ya bar Jam’iyyar. Yanzu Arobo da sauran Lauyoyi sun yi taron dangi su na kalubalantar Gwamnan.

Kafin a dage shari’ar, Lauyan da ke kare Abokan hamayyar Gwamnan watau Roland Otaru ya fadawa Alkali Mohammed Dattijo cewa wadanda su ka zabi Tambuwal a matsayin ‘Dan takarar APC a zaben 2014 ba su cancanta ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng