Dage shari’ar Dakingari zuwa 2019 ya sabawa dokar Kasa – Transparency IT

Dage shari’ar Dakingari zuwa 2019 ya sabawa dokar Kasa – Transparency IT

- Babban Kotun Tarayya ta dage shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kebbi

- Alkalin Kotun ya bada belin su Usman Dakingari kan kudi Miliyan 50

- Kungiyar Transparency IT tace dage zaman da Kotu tayi bai halatta ba

Dage shari’ar Dakingari zuwa 2019 ya sabawa dokar Kasa – Transparency IT
An bada belin Saidu Dakingari da wasu mutum 2 a Kotu
Asali: Depositphotos

Mun samu labari cewa babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Kebbi a cikin Jihar Kebbi ya bada belin Usman Nasamu Dakingari wanda aka garkame a gidan yari bisa zargin yin sama da wasu Miliyoyin kudi a Ranar Litinin dinnan.

Alkali mai shari’a Sunday Onu ya bada belin tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Usman Dakingari da kuma wasu mutane 2 da ake zargi da hannu wajen satar Miliyan 450 a 2014. Sauran mutanen su ne: Rabiu Kamba da kuma Sunday Dogonyaro.

KU KARANTA: An kalubalanci Shugaba Buhari ya binciki wasu na gefen sa

Yanzu dai Alkali Onu ya bada izinin a karbi belin tsohon Gwamnan a kan kudi Naira Miliyan 50. Alkalin ya kuma dage shari’ar har sai farkon Watan Fubrairun shekara mai zuwa. Masu tuhumar Dakingari dai sun nuna ba haka su ka so ba.

Kungiyar TransparencyIT da ke Najeriya tayi Allah-wadai da wannan mataki da Alkalin Kotu Sunday Onu ya dauka. Kungiyar mai bin shari’ar da ake yi da wadanda ake zargin sata a Najeriya tace bai dace a daga shari’ar zuwa 2019 ba.

TransparencyIT tace dokar ACJA watau ‘Administration of Criminal Justice Act’ ba ta bada damar a dage shari’a na fiye tsawon fiye makonni 2 ba. Kungiyar tace dage zama har zuwa farkon badi ya sabawa sashe na 396 ba sabuwar dokar ACJA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: