Gwamna Ganduje ya tallafawa Matasa 1850 a jihar Kano

Gwamna Ganduje ya tallafawa Matasa 1850 a jihar Kano

Za ku ji cewa, akalla kimanin Matasa 1850 ne yayyafin arziki ya kai gare su, yayin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tallafin dogaro da kai ta hanyar koyar da sana'o'i da kuma makamar aiki.

Ko shakka ba bu a halin yanzu Matasa 1850 ke amfanar tallafin gwamnan jihar Kano yayin da kamfanin kera Motoci samfurin Peugeot ya yaye Matasa 150 da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin horas da su akan sana'ar gyaran Mota.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Ganduje ya sha alwashin bayar da tallafin dogaro da kai ga fiye da Matasa miliyan 1 gabanin kammala wa'adin mulkin sa karo na farko bisa kujerar gwamnatin jihar.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne cikin jawabansa ga Matasa 1850 da aka horas yayin bikin yaye su da aka gudanar a fadar gwamnatinsa da ke shiyyar Nasarawa da kuma Tarauni a Kanon ta Dabo.

Gwamna Ganduje ya tallafawa Matasa 1850 a jihar Kano
Gwamna Ganduje ya tallafawa Matasa 1850 a jihar Kano
Asali: Twitter

A cewarsa, wannan shiri na bayar da tallafin dogaro da kai ga Matasa kudiri ne na gwamnatin su domin kawo rangwami na talauci, dakile zaman kashe wando da kuma samar da ayyukan yi da sana'o'i a fadin jihar.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancinsa ta samu nasara mai girman gaske wajen sanya hannun jari ta hanyar bayar da tallafin dogaro da kai ga Matasa a fannikan sana'o'i da dama.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun yi garkuwa da Fasinjoji 18 a jihar Ribas

Cikin na sa jawaban, Ministan kwadago na kasa yayin halartar taron a fadar gwamnatin Kano, Dakta Chris Ngige, ya yabawa kwazon gwamna Ganduje dangane da nasarori da gwamnatin sa ta cimma a bisa tafarki na samar da abin dogaro da kai ga Matasa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayar da lasisi tare da cewa ba bu laifi ga Masoya da suka haura shekaru 18 a duniya idan su tara da juna cikin Motocin su, inda ta ce hakan bai sabawa dokar kasa ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel