Wasu na-hannun daman Shugaba Buhari su na tsula tsiya – PDP

Wasu na-hannun daman Shugaba Buhari su na tsula tsiya – PDP

Mun samu rahoto cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito yayi wa Duniya jawabi game da zargin da ke kan wuyoyin wasu manyan na-kusa da shi a halin yanzu.

Wasu na-hannun daman Shugaba Buhari su na tsula tsiya – PDP
Jam’iyyar PDP ta zargi Buhari da daurewa rashin gaskiya gindi
Asali: Depositphotos

Babbar Jam’iyyar hamayyar ta nemi Shugaba Buharu yayi bayanin kudin da ake zargi ‘Yan siyasa sun tara masa ta hannun Mai dakin sa. Ana zargin wasu mutane sun tara kudin da su ka haura Biliyan 2.5 da sunan Hajiya Aisha Buhari.

Shugaban Jam’iyyar adawa na Kasar, Prince Uche Secondus ya kalubalanci Shugaba Buhari ya soma binciken na kusa da shi, idan har da gaske mutum ne shi mai gaskiya. PDP tace wasu na-hannun daman Buhari su na tafka tsiya.

Uche Secondus ya koka da yadda Jami’an Hukumar DSS su ka takawa wata Baiwar Allah mai suna Amina Mohammed burki bayan tayi kokarin tona asirin irin barnar da wasu da ke kusa da Shugaban Kasa Buhari su ke tafkawa a kasar.

KU KARANTA: Buhari ya sa Ministocin Najeriya sun kyalkyace da dariya a taron FEC

Sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan, yayi kira ga Shugaba Buhari yayi bincike game da abubuwan da wannan Baiwar Allah Amina Mohammed ta fada domin a bankado barnar da wasu tsirarru su ke yi a cikin Gwamnatin nan.

Jam’iyyar ta kuma nemi a fito da rahoton binciken da aka gudanar game da tsohon Dogarin Matar Shugaban kasa watau Baban-Inna wanda aka kama yana karbar kudi daga hannun ‘Yan siyasa da manyan ‘Yan kasuwa da sunan Uwargidar.

PDP ta kuma yi magana game da Dala Biliyan 1 da aka cire da sunan yakin Boko Haram da kuma Tiriliyan 11 da ake tunani sun bata a Kamfanin NNPC. Haka kuma ana zargin cewa an wawuri fiye da Biliyan 50 daga kudin ‘Yan gudun Hijira.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel