An kashe mutane 7, 16 sun jikkata a rikicin matsafa daya barke a garin Legas

An kashe mutane 7, 16 sun jikkata a rikicin matsafa daya barke a garin Legas

Akalla mutane bakwai ne suka rigamu gidan gaskiya a wani rikici daya barke a garin Legas na jahar Legas tsakanin wasu kungiyoyin matsafa biyu da basa ga maciji da juna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan rikici ya faru ne a wata unguwa dake cikij garin Legas Badia Ijora, inda matasan kungiyar matsafa ta Aye da na Eiye suka far ma junansu ba kakkautawa, a dalilin haka ne mutane bakwai suka mutu.

KU KARANTA: An kwace kujerar wani dan majalisa bayan ya yi wankan tsarki daga APC zuwa PDP

Sai dai baya ga asarar rayukan da aka yi, rikicin yayi sanadiyyar ji ma wasu mutane goma sha shida rauni daban daban, haka zalika sun tafka ma jama’an yankin asarar dukiyoyi da suka kai na miliyoyin nairori, kai wasu matasan ma sai duka afka gidaje da shagunan mutane suka yi musu sata.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa matsafan sun yi amfani da makamai da dama wajen kai ma junansu farmaki, da suka hada da bindigu, adduna, gatari, manya manyan dutwasu, da makamantansu.

Daga cikin mutanen da rikicin ya rutsa dasu har yayi sanadiyyar mutuwarsu akwai wani mutumi dake aiki a kamfanin inshore ta Leadway, mai suna Muyideen Saka, da wani mutumi Wasiu Ajani mazaunin gida mai lamba 42 titin Baale.

Sai dai akwai wasu matasa da aka halaka a cikin wannan rikici, Ejima da Noah, wanda shaidun gani da ido suka tabbatar da sune suka janyo rikicin a wannan unguwar, kuma yansanda sun samu nasarar damke mutane goma sha shida dake da hannu cikin lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: