Babu gudu babu ja da baya: Malaman kwalejojin kimiyya da fasaha zasu jefar da alli a gobe

Babu gudu babu ja da baya: Malaman kwalejojin kimiyya da fasaha zasu jefar da alli a gobe

Kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta Najeriya, ASUP, ta sanar da hukuncin data yanke na shiga yajin aiki har sai illa masha Allahu daga karfe sha biyu na daren Laraba, kamar yadda shugaban kungiyar, Usman Dutse ya tabbatar.

Legit.com ta ruwaito Duste ya sanar da haka ne a yayin ganawa da yayi da kamfanin dillancin labarun Najeriya a garin Legas, inda yace babu gudu babu ja da baya sai sun jefar da alli tunda dai gwamnati ta gaza cika alkawurran data daukan ma kungiyar a shekarar 2009 da 2017.

KU KARANTA: Kwankwaso ya karbi sabbin mabiya daga masana’antar Kannywood

Babu gudu babu ja da baya: Malaman kwalejojin kimiyya da fasaha zasu jefar da alli a gobe
Kungiyar ASUP
Asali: Twitter

“Zamu fara yajin aikin ne daga gobe Laraba, Minista ya gayyacemu tattaunawa a ranar 17 ga watan Disamba, amma ban san abinda za’ayi a taron ba har sai mun hadu a ranar, amma fa ba zamu sassauta ba har sai an cika mana duk alkawurran da aka daukan mana.” Inji shi.

Bugu da kari, shugaban ASUP, ya kara da cewa daga karfe sha biyu na daren Laraba duk wani malamin dake karkashin kungiyarsu ya daina aiki, kuma sun aika ma shuwagabannin rukuni rukuni dasu tabbatar dukkanin malaman dake rukuninsu sun bi umarnin uwar kungiya

Sai dai Malam Duste ya bayyana cewa duk kokarin da suka yi na ganin gwamnatin tarayya da ministan ilimi Adamu Adamu sun aiwatar yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamnati da ASUP a shekarar 2009 yaci tura, hakan ne ya tilasta musu daka yajin.

Daga cikin bukatun da ASUP ke kira ga gwamnati ta biya musu akwai nuna halin ko-in-kula da sake tattaunawa akan yarjejeniyar 2010, rashin biyan CONTISS 15 ga kananan malamai, rashin biyan malamai kudin karin girma, rashin daukan sabbin Malamai.

Sauran sun hada da rashin biyan albashin malaman kwalejojin kimiyya da fasaha a jihohi da dama, rashin aiwatar da rahoton NEEDS na shekarar 2014, cin zarafin Malamai da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng