Iyalan tsofaffin ma’aikatan NITEL su 500 da suka mutu sun samu N1,500,000,000 daga Buhari

Iyalan tsofaffin ma’aikatan NITEL su 500 da suka mutu sun samu N1,500,000,000 daga Buhari

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biya tsofaffin ma’aikatan kamfanin sadarwa ta Najeriya, NITEL/MTEL su dari biyar da suka mutu hakkokinsu da suka kai naira biliyan daya da miliyan dari biyar (N1,500,000,000).

Gwamnatin ta mika wadannan kudade ga iyalan mamatan ne ta hannun hukumar wucin gadi dake dake kula da yan fansho wato PITAD dake karkashijn jagorancin jarumar mace Sharon Ikeazor.

KU KARANTA: Tsofaffin ma’aikata zasu shana: Buhari ya yi ma yan fansho karin kudi da kashi 33

Majiyar Legit.com ta ruwaito PITAD ta kammala tantance iyalan mamatan da suka yi aiki da kamfanin NITEL/MTEL a baya amma har suka rasu ba tare da sun samu hakkokinsu ba, wanda tace adadinsu ya kai dari biyar.

Iyalan tsofaffin ma’aikatan NITEL su 500 da suka mutu sun samu N1,500,000,000 daga Buhari
Sharon
Asali: UGC

Itama da take nata jawabin, uwargida Sharon tace sun samu nasarar biyan iyalan hakkokin yan uwansu ne sakamakon jajircewa da suka yi wajen tantance sunayen iyalan da mamatan suka rubuta a takardun aiki a matsayin yan uwansu.

Daga karshe ta bada tabbacin duk wani dan fansho da hakkin biyansa hakkokinsa ya rataya a wuyan hukumar PITAD zai samu kudadensa nana bada jimawa, koda kuwa sun mutu, iyalansu zasu samu kudaden yan uwan nasu.

A wani labarin kuma hukumar PITAD ta fara biyan biyan tsofaffin ma’ikata kudadensu na fansho na watanni shida har ma da karin kashi Talatin da uku da Buhari ya amince ayi.

PITAD ta fara biyan wannan karin kudin ne a ranar Litinin 3 ga watan Disamba, kamar yadda sakataren kungiyar yan fansho ta kasa, Actor Zal ya bayyana a ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba, kamar yadda shugaban hukumar fansho, PITAD, Sharon Ikeazor ta tabbatar musu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng