Kallo ya koma sama: An tafka sata a majalisun dokokin Najeriya

Kallo ya koma sama: An tafka sata a majalisun dokokin Najeriya

Maganar dake daukar hankulan jama’a a yanzu shine yadda tsaro ya tabarbare a majalisun dokokin Najeriya wanda haka yasa suka zama tamkar dandalin sace sace, inda mutane da dama suka bada rahoton sace musu batiran motoci, har ma da motar a wasu lokutan.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wani dan jarida yana bayyana cewa barayi na cin karensu babu babbaka a harabar majalisar, inda suke satan batiran motoci tare da barnata motocin, domin kuwa shima dan jaridar ya fuskanci wannan matsala.

KU KARANTA: Ba zan taba yarda ayi ma Buhari hawan kawara a majalisar dattawa ba – Inji Sanata

“Da misalin karfe 11:30 na safe na ajiye motata kirar CRC a wajen ajiyan motoci, amma da na dawo wajen motar da misalin karfe 6 na yamma, sai na tarar an balle min kofar bonet tare da dauke min batirin motar.

“Na kai kara ga ofishin Yansanda dake majalisar, amma babu wani mataki da suka dauka, ko irin su dan tafi zuwa wajen motar don gane ma idanuwansu ma basu yi ba.” Inji dan jaridan da lamarin ya shafa.

Wannan dai shine kukan da yan jaridu da ma sauran ma’aikatan majalisa ke yi, kuma duk da wannan koke da aka dade ana yi babu wani sauki da aka samu sakamakon Yansandan dake gadin majalisar sun gaza kawo karshen matsalar.

Shima wani dan jarida da lamarin ya faru da shi, Mudashiru Atanda ya bayyana cewa; “A ranar juma’a na ajiye mota a bayan ginin majalisun dokoki, da lokacin sallar juma’a tayi, sai na tafi don shiga motata na wuce Masallaci.

“Amma isata inda na ajiye motar keda wuya sai na tarar da bonet dina a wangame, amma sai nayi tunanin nine ban rufeshi da kyau ba, don haka sai na daga shi don na rufeshi da kyau, a lokacin ne na lura ashe har an sace min batir.” Inji shi.

Sai dai ma’aikatan tsaro dake majalisar sun bayyana cewa shawo kan wannan matsala na da wuyan gaske, saboda babu isassun kayan aiki a majalisar, musamman ma na’urorin daukan hoto na majalisar duk sun lalace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel