Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo zai gana da ‘Yan kasuwan Jamus

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo zai gana da ‘Yan kasuwan Jamus

- Mataimakin Shugaban kasan Najeriya zai yi tafiya zuwa Kasar Jamus an jima

- Yemi Osinbajo zai yi magana ne game da kasuwancin Najeriya a Birnin Berlin

- Farfesa Osinbajo zai kuma tattauna game da tsare-tsaren Gwamnatin Buhari

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo zai gana da ‘Yan kasuwan Jamus
Fadar Shugaban kasa tace Mataimakin Shugaban kasa yayi tafiya
Asali: Facebook

Mun samu labari daga Fadar Shugaban kasa cewa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi tafiya zuwa Kasar Jamus a a jiya Lahadi 9 ga Watan Disamban nan. Osinbajo zai yi tafiya ne zuwa Birnin Berlin ta Kasar Turai.

Mataimakin Shugaban kasar zai gana da manyan ‘Yan kasuwar Birnin Berlin a yau dinnan. Ofishin Jakadancin Najeriya a Kasar Jamus da kuma wata Kungiya ta ‘Yan kasuwan Afrika da ke Kasar Turan su ka shirya wannan zama.

Laolu Akande wanda yake magana da yawun bakin Mataimakin Shugaban kasar yace Osinbajo zai tattauna ne game da irin saukin da aka samu wajen harkar kasuwanci yanzu a Najeriya da zuwan Gwamnatin Shugaba Buhari.

KU KARANTA: Babban limamin Yarbawa na cikin Garin Sokoto ya mutu

Idan ba ku manta ba, a ziyarar da Shugabar Kasar Jamus Angela Merkel ta kawo Najeriya, ta bayyana cewa Kasar ta za ta hada kai da Najeriya a harkar zuba hannun jari da kasuwanci da kuma bangaren noma da kimiyya da fasaha.

Laolu Akande yace bayan nan kuma Osinbajo zai karaso zuwa Landan inda zai gana da wata Kungiya domin jawo hankalin su da su zuba hannun jari a Afrika. A karshe Osinbajo zai wakilci Buhari a wani taro da za ayi a Kasar Masar.

Farfesa Yemi Osinbajo yana cikin wadanda za su yi jawabi a taron da za ayi a Masar a madadin Shugaban Najeriya. Mataimakin Shugaban kasar da Mukarraban sa za su dawo gida ne a Ranar Alhamis 13 ga wannan Watan na Disamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel