Magu ya fadi 'yan siyasar da ya dace 'yan Najeriya su zaba

Magu ya fadi 'yan siyasar da ya dace 'yan Najeriya su zaba

- Mukadashin hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya shawarci 'yan Najeriya su zabi adalan shugabanin ba tare da la'akari da jam'iyya ba

- Magu ya ce ya zama dole 'yan Najeriya su zabi shugabani masu gaskiya da adalci saboda 'ya'yan mu da jikokin mu su kaucewa kuskuren da mu kayi

- Mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawar ya kuma ce barayin gwamnati ba su da mafa a Najeriya a halin yanzu

Ibrahim Magu, mukadashin shugaban hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC ya yi kira da 'yan Najeriya su zabi adalan shugabanni ba tare da yin la'akari da jam'iyyun siyasar da suke takarar a karkashin su ba a 2019.

Magu ya fadi 'yan siyasar da ya dace 'yan Najeriya su zaba

Magu ya fadi 'yan siyasar da ya dace 'yan Najeriya su zaba
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya fadi abinda gwamnatinsa ba za ta yarda da shi ba idan aka zabe shi

"Kada ku zabi duk wani wanda ba adali bane ko a wace jam'iyya ya fito takara. Ya kamata mu zabi mutane masu gaskiya wanda suke kishin kasarmu. Ya kamata mu kare yaran mu da jikokin mu daga kura-kuren da mu kayi," inji Magu.

Ya kuma ce a yanzu, barayin gwamnati ba su da mafaka a Najeriya.

Magu ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a wajen wani taron yaye jami'an Compliance Institute of Nigeria, (CIN) a Legas. Ya shaidawa jami'an hukumar cewa suma masu yaki da rashawa ne a Najeriya.

"Kuma masu yaki da rashawa ne, bai kamata ku barwa hukumomin yaki da rashawa aikin su kadai ba. Nauyin yaki da rashawa ya rataya a wuyan dukkan mu ne, ya ma kamata 'yan Najeriya su dauki yaki da rashawa kamar ta su ce."

Shugaban hukumar, Pattison Boleigha ya bayyana taron a matsayin wata babban nasara cikin yaki da rashawa da magance ta'addanci da kuma koyar da 'yan Najeriya tarbiya.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewar hukumar ta EFCC za ta sanya idanu a kan kudaden da 'yan siyasa ke kashewa wajen yakin neman zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel