An kwace katin zabe 700 daga hannun wasu bakin haure

An kwace katin zabe 700 daga hannun wasu bakin haure

A cigaba da aikin hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) na ganin cewar bakin haure basu kada kuri'a a zaben 2019 ba, shugaban hukumar na kasa, Muhammad Babandede, ya sanar da cewar sun yi nasarar kwace katunan zabe kimanin 700 daga hannun wasu bakin haure dake zaune a Najeriya.

Mohammed Babandede, babban kwanturola na hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), ya jami'an hukumar sa sun yi kwace katin zabe fiye da 700 daga hannun bakin haure.

Da yake gabatar da jawabi a yau, Asabar, yayin wani taron karrama jami'an hukumar NIS da suka nuna kwazo na musamman a aiki, Babandede ya bayar da tabbacin cewar zasu yi iya bakin kokarinsu na ganin cewar 'yan Najeriya ne kadai suka kada kuri'a a zaben 2019.

An kwace katin zabe 700 daga hannun wasu bakin haure
Katin zabe
Asali: UGC

Babban kwanturolan ya kara da cewa yanzu haka ya ware wasu jami'ai na musamman da zasu ke tantance bakin haure domin gano masu katin zabe da kuma kwace shi daga hannunsu.

DUBA WANNAN: 2019: Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya bawa bawa Buhari gudunmawar motoci 110

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2019. Zaben 'yan majalisun tarayya ne zai biyo bayan na shugaban kasa, kamar yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) ta fitar a jadawalinta na gudanar da zaben shekarar ta 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel