Badakalar Diezani: EFCC ta damke wasu 'yan siyasa 2 a jihar Adamawa
- Badakalar rashawa ta tsohuwar Ministan Man fetur Diezani, ta shafi wasu manyan 'yan siyasa biyu a jihar Adamawa
- Hukumar EFCC ta cafke da wasu 'yan siyasa biyu kan zargin alakar su da badakalar tsohuwar Ministan Man fetur
- EFCC ta gurfanar da ababen zargin a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin Yola na jihar Adamawa
Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta gurfanar da wasu jiga-jigan 'yan siyasa biyu a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Hukumar ta gurfanar da 'yan siyasar biyu gaban Mai Shari'a Abdulaziz Anka, na babbar Kotun tarayya da ke birnin Yola a jihar Adamawa. Ana tuhumar su da laifukan zamba da kuma karkatar da dukiyar gwamnati zuwa ga bukatun kansu.
Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, man 'yan siyasar biyu sun hadar da; Joel Madaki, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar da kuma Felix Tagwami, tsohon jagoran kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Mallam Nuhu Ribadu a shekarar 2015 da ta gabata.
Binciken da hukumar EFCC ke ci gaba da aiwatarwa kan tsohuwar Ministan ma'adanan man fetur, Diezani Alison Madueke, ya alakanta 'yan siyasar biyu da da zargin rashawa makudan dukiyar gwamnati ta $115m.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata, hukumar EFCC ta dakumo tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Dakingari bisa zargin hannunsa cikin badakalar rashawa ta tsohuwar Ministan gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Bayelsa ta sha alwashin hukunta wadanda suka haddasa tarzoma a Zaben 2015
Hukumar EFCC na zargin tsohon gwamnan da karbar Naira miliyan 145 cikin kudaden da tsohuwar Ministan ma'adanan man fetur da wawusa a cikin dukira al'umma ta kasar nan.
Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, hukumar mai yaki da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero a gaban Kuliya, bisa zargin sa da babakere gami da wawushe dukiyar al'umma ta kimanin N700m.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng