Atiku ya fadi siffar irin gwamnatin da yake fatan kafa wa

Atiku ya fadi siffar irin gwamnatin da yake fatan kafa wa

Dan takarar shugabancin kasa na babban jam'iyyar adawa ta PDP ya jadada cewa a shirye ya ke ya yi aiki tare da sauran jam'iyyun siyasa domin tafiyar da gwamnati bayan ya yi nasarar lashe zabe. Ya ce dama PDP ba ta kyamar gwamnatin hadin kai tun kafa ta a shekarar 1998.

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples democratic party, PDP, ya ce a shirye ya ke domin kafa gwamnatin hadin kai.

Ya fadi hakan ne a ranar Juma'a a Abuja yayin da ya ke ganawa da hadakan jam'iyyun siyasan Najeriya CUPP da ke dauke da jam'iyyun siyasa 45 da suka goyi bayansa a matsayin dan takarar shugabancin kasarsu.

Atiku ya fadi siffar irin gwamnatin da yake fatan kafa wa

Atiku ya fadi siffar irin gwamnatin da yake fatan kafa wa
Source: Facebook

Ya ce jam'iyyar PDP tayi imani da gwamnatin hadaka tare da damawa da dukkan 'yan Najeriya ba tare da la'akari da jam'iyyun siyasar da suke ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1998.

DUBA WANNAN: Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

"Zan cigaba da tsarin gwamnatin hadaka. Akwai ayyuka sosai da za muyi tare. Bai kamata mu koma gefe guda mu zauna ba muce kawai mun goyi bayan wani dan takarar," a cewar Atiku.

Dan takarar shugabancin kasar ya mika godiyarsa ga CUPP saboda mara masa baya da su kayi inda ya ce ba zai taba manta wannan karamcin da su kayi masa ba.

"Ba kuyi kuskure ba saboda tun lokacin da aka kafa jam'iyyar PDP a shekarar 1998, jam'iyyar tana da ra'ayin gwamnatin hadaka," inji shi.

Wani jigo a tafiyar, Cif Timi Ikimi ya ce aikin da ke gabansu abu ne mai wahala amma mambobin CUPP sun dauki alkawarin ba za su gajiya ba.

Alhaji Saidu Bobboi, shugaban jam'iyyar Kowa Party na kasa ya ce jam'iyyarsa ba za tayi watsi da CUPP ba kuma tana nan kan bakar ta goyon bayan Abubakar a matsayin dan takarar shugabancin kasa kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel