2019: Ku bawa Buhari tukwuici - Gwamnan APC ga masu cin moriyan Npower

2019: Ku bawa Buhari tukwuici - Gwamnan APC ga masu cin moriyan Npower

- Gwamna Oluwarotimi na jihar Ondo ya yi kira ga masu amfana da Npower su sakawa Buhari ta hanyar kada masa kuri'a a 2019

- Gwamna Akeredolu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun cika alkawurran da suka yiwa matasa

- Gwamnan ya kuma shawarci gwamnatin tarayya ta cigaba da fadada shirin domin bawa wasu matasan daman amfana da shirin

2019: Ku ba Buhari tukwuici - Gwamnan APC ga masu cin moriyan Npower

2019: Ku ba Buhari tukwuici - Gwamnan APC ga masu cin moriyan Npower
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya yi kira ga masu cin moriyan shirin Npower a dukkan sassan Najewriya su sakawa shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa ta hanyar sake zabensu a babban zaben 2019.

Gwamnan ya yi wannan kirar ne a wata taro da ya yi tare da masu amfana da shirin Npower na jihar Ondo a garin Akure, ya ce sake zaben shugaba Buhari zai sanya wasu sabbin mutanen su sake samun damar shiga shirin da ke inganta rayuwan al'umma.

DUBA WANNAN: Buhari sai ya fadi, in ji Atiku

Afolabi Imoukuede, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan samar da ayyuka shine ya jagoranci masa amfana da shirin na Npower zuwa dakin taro na Gani Fawehinmi da ke Akure bayan gudanar da wata tattaki na nuna goyon bayan Buhari da Osinbajo.

Akeredolu ya ce shirin ya bawa matasa masu dimbin yawa damar cin moriyar baiwan da Allah ya yi musu kuma ya bukaci gwamnati ta cigaba da shirin.

Ya ce shugaban kasar da mataimakinsa sun cika alkawurran da suka yiwa matasan Najeriya.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da bayar da hadin kai domin samun nasara a dukkan shirye-shiryen inganta rayuwar al'umma da gwamnatin tarayya da kirkira a jihar sa.

Mataimakain shugaban kasar ya ce baya ga kudaden da ake baiwa masu amfana da shirin Npower a duk wata, shirin na baiwa matasa daman amfana da wasu abubuwan da suka ki albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel