Gwamnatin jihar Yobe tayi feshin maganin gafiyoyi a makabartu

Gwamnatin jihar Yobe tayi feshin maganin gafiyoyi a makabartu

Kwamitin da jihar Yobe ta kafa a kan tsaftar muhalli ya fara shara da feshin magani domin kawar da ciyawa da dangin halittun kadangare, kamar su jaba, gafiya da sauransu.

Da yake bayani a kan wannan aiki, Abubakar Ali, mataimakin gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin tsaftar muhallin, ya ce ruwan damuna ya haifar da girman bishiyoyi da rassansu ke fadowa suna rusa kabarbura, a saboda haka akwai bukatar a yi gyara a makabartun.

"Hakan ne yasa muka tattaro dukkan 'yan kwamitin muhalli domin gyara makabartu da yin feshin magani," a kalaman mataimakin gwamnan.

Gwamnatin jihar Yobe tayi feshin maganin gafiyoyi a makabartu

Ibrahim Gaidam
Source: UGC

Ali ya kara da cewar ma'aikata sun sha wahala sosai wajen gyaran makabartu 7 saboda yawan ciyawa da bishiyoyi da suka lullube hatta hanyar da jama'a da zasu bi.

DUBA WANNAN: An kulle mahaifina a kurkuku saboda ya yi kokarin hana ni zuwa makaranta - Atiku

Kazalika ya mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, bisa goyon bayan da yake bawa kwamitin na tsaftace muhalli.

Idi Wadaina, shugaban hukumar kula da tsaftar muhalli a jihar Yobe, ya ce sun shiga cikin aikin tare da leburori ne domin jawo hankalin 'yan sa-kai, su shigo a yi aikin tare da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel