Atiku ya dauki alkawarin fara yiwa Najeriya kwaskwarima cikin watanni 6

Atiku ya dauki alkawarin fara yiwa Najeriya kwaskwarima cikin watanni 6

Dan takarar shugbancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin fara gyaran tsarin rabon arzikin kasa cikin watanni shida da rantsar da shi idan har ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Atiku ya yi wannan alkawarin ne a ranar Alhamis a garin Ibadan yayin kadamar da yakin neman zabensa na yankin Kudu maso yamma a kasar.

Ya yi alkawarin zai yi amfani da kwarewar da ya ke dashi a fannin kasuwanci domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Atiku ya dauki alkawarin fara yiwa Najeriya kwaskwarima cikin watanni 6
Atiku ya dauki alkawarin fara yiwa Najeriya kwaskwarima cikin watanni 6
Asali: Facebook

Atiku ya yi alkawarin kawo tsare-tsare da za su inganta harkar ilimi a kasar wadda dama an san mutanen yankin da kwazo wajen neman ilimi.

DUBA WANNAN: Ba wan, ba kanin: Jam'iyyar AA taki amincewa da surukin Rochas

A jawabinsa, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Uche Secondus ya bayyana farin cikinsa ga dimbin al'ummar da suka fito kwansu da kwarwata domin tarbarsu wadda ya ce alama ce da ke nuna mutanen suna son canji.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa dukkan 'yan takarar majalisun tarayya, na jihohi da kuma na gwamna a jam'iyyar PDP daga yankin sun hallarci taron kaddamar da yakin neman zaben.

Yan takarar gwamna da suka hallarci wajen sun hada da Buruji Kashamu daga jihar Ogun, Jimi Agbaje daga jihar Lagos da Seyi Makinde daga jihar Oyo.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel suma sun samu damar hallartar taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel