Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari

Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari

A yau Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ko shakka ba bu ya na da cikakkiyar fahimta gami da masaniya ta muradi da kiraye-kiraye na bukatun al'ummar kasar nan da yana da cikakken yakini fatan su za ya tabbata.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya kuma bayar da tabbacin sa dangane da yadda sakamakon babban zabe na 2019 za ya zamto tamkar haske na madubin dubawa da al'ummar kasar nan suka burata.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne cikin fadarsa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya yayin karbar sabon jakadan kasar Finland zuwa Najeriya, Dakta Jyrki Juhani Pulkkinen.

Cikin wata sanarwa ta kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya bayyana cewa, 'yan Najeriya na da cikakken 'yanci na zaben shugabanni a matakai da kujerun siyasa daban-daban yayin zabe na 2019 kuma dukkanin wani yunkuri za ya tabbata na inganta babban zabe na kasa.

Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari

Sakamakon Zaben 2019 zai haskaka kudirin al'ummar Najeriya - Buhari
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya kuma taya murna ga kasar Finland dangane da cikar ta shekaru 101 da samun 'yanci kai a yau 6 ga watan Dasumba, inda ya yabawa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da kasar Najeriya musamman a faninkan fasahar sadarwar ta zamani da kuma harkokin ilimi.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya kuma karamma sabon jakadan kasar Faransa zuwa Najeriya, Mista Jerome Pasquier, inda ya sake jaddada farin cikinsa dangane da ziyartar kasar nan da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya aiwatar watanni kadan da suka gabata.

Baya ga jakadan kasar Finland da kuma na Faransa, shugaba Buhari a fadarsa ta Villa ya kuma karbi sabon jakadan kasar jamhuriyyar Czech, Mista Marek Skolil, inda ya sha alwashin inganta dankon zumunta a tsakanin kasashen biyu.

KARANTA KUMA: Dakaru sun dakile wani sabon hari na Boko Haram a jihar Borno

Mista Skolil ya kuma bayar da tabbacin goyon bayan kasar sa ga shugaba Buhari wajen bayar da duk wata gudunmuwa wajen yakar ta'addanci a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa ba za ya sake korafi kan gwamnatocin baya ba da kuma matsalolin da suka haddasawa kasar nan da a halin yanzu ta ke ci gaba da fuskanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel