Dakaru sun dakile wani sabon hari na Boko Haram a jihar Borno

Dakaru sun dakile wani sabon hari na Boko Haram a jihar Borno

Za ku ji cewa Hukumar sojin kasan Najeriya, ta samu nasarar dakile wani sabon hari na mayakan Boko Haram, inda ta salwantar da rayuwar dan ta'adda guda yayin da dama suka arce da raunuka na harsashin bindiga a jihar Borno.

Kakakin hukumar sojin na kasa, Birgediya Janar Sani Usman, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa da ya bayyana cewa, hukumar ta kuma samu nasarar cafke 'yan ta'adda biyu yayin fafatawa ta barin wuta.

Dakaru sun dakile wani sabon hari na Boko Haram a jihar Borno

Dakaru sun dakile wani sabon hari na Boko Haram a jihar Borno
Source: Depositphotos

Janar Sani ya bayyana cewa, dakarun sojin tare da hadin gwiwar dakarun tsaro na sa kai a ranar Talata 4 ga watan Dasumba, sun samu nasarar yiwa 'yan ta'adda kwanton bauna a yankunan Yachida, Korongelen, Bombula da kuma Forfor da ke karkashin karamar hukumar Damboa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, baya ga wannan nasara, hukumar sojin ta kum samu nasarar kai hannunta kan miyagun makamai na 'yan ta'adda da bayan tura ta kai bango ta sanya suka arce ba bu shiri.

KARANTA KUMA: ASUU: Gwamnatin tarayya za ta gana da Malamai kan yajin aiki a ranar Litinin

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, dakaru 2 na hukumar sojin sun jikkata yayin fafatawa da 'yan ta'adda inda a motar agaji ta yi gaggawar garzaywa da su asibitin dakaru da a halin yanzu suke ci gaba da samun kyakkyawar kulawa.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar tsaro ta dakaru ta aika da karin adadi na dakarun soji zuwa garin Jakana inda 'yan ta'adda ke shirin yiwa kawanya a jihar Borno.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel