Har yanzu kaso mafi tsoka na kudin da aka sace na cikin Najeriya - Magu

Har yanzu kaso mafi tsoka na kudin da aka sace na cikin Najeriya - Magu

- Mukadashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya ce 60% na kudaden da manyan gwamnati suka sata yana Najeriya

- Magu ya kuma ce akwai dallan Amurka miliyan 300 a kasar Ingila amma har yanzu ba a dawo da shi Najeriya ba

- Ya kuma ce kotun Najeriya ba wai ta bayar da umurnin a kamo tsohuwar ministan man fetur bane domin tayar da husuma tsakanin kasashen biyu

A kalla kashi 60 cikin dari na kudaden da tsaffin ma'aikatan gwamnati suka sace daga asusun gwamnati suna nan a Najeriya baya da $300 miliyan da ke Jersey Island a kasar Ingila wadda har yanzu ba a karbo ba inji mukadashin hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Har yanzu kaso mafi tsoka na kudin da aka sace na cikin Najeriya - Magu

Har yanzu kaso mafi tsoka na kudin da aka sace na cikin Najeriya - Magu
Source: Depositphotos

Ya kuma ce bukatan da gwamnatn Najeriya ta mika ga kasar Ingila na dawo da tsohuwar minitan man fetur na Najeriya, Mrs Diezani Alison-Madueke domin ta fuskanci hukunci ba anyi bane domin a rikici tsakanin kasashen biyu.

DUBA WANNAN: Oshiomhole na da mugun nufi a kan APC - Rochas

Magu ya ce hukumar EFCC za tayi biyaya ga umurnin kotu da ta bata na gabatar da tsohuwar ministan a gaban kuliya a cikin kwanaki uku.

Ya kara da cewa: "60% na cikin kudaden da aka sace suna nan a Najeriya. Hakan yasa na ke bukatar mu hada gwiwa domin mu kama su. Nawa ne adadin ma'aikatan EFCC? Akwai al'umma 180 miliyan a Najeriya, guda nawa ke aiki a Najeriya? Ina rokon dukkan hukumomin tsaro su hada hannu da mu."

"Za muyi biyaya ga umurnin kotu kamar yadda muka saba yin hakan a baya saboda babu wani lokaci da muka ki biyaya ga umurnin kotu. Idan ba muyi biyaya da umurnin kotun ba hakan na nufin muna da dalilan kaukaka kara kan umurnin na kotu kuma muna da ikon yin hakan.

"Sa'o'i 72 ya yawa domin kamo Diezani amma ta yaya zan kamo ta yayinda tana kasan waje inda wasu hukumomin tsaron ke bincikarta. Wannan shine matsalar da muke fuskanta idan ba hakan ba, da mun ganta za mu kama ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel